Mahara sun sace shugaban jam’iyyar PDP a Edo
Maharan sun yi awon gaba da shi, yayin da yake kan hanyar komawa gidansa da ke Benin.
Wasu da ake kyautata zaton ‘yan bindiga ne, sun yi awon gaba da shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Edo, Mista Tony Aziegbemi.
Bayanai sun ce an ɗauke Mista Azeigbeme ne a kan hanyarsa ta komawa gidansa da ke Benin, babban birnin jihar.
Maharan sun tare shugaban PDPn da wasu motoci guda biyu kirar Toyota Corolla da misalin karfe 11 na dare, inda suka yi awon gaba da shi.
Rahotanni sun bayyana cewa ya baro gidan gwamnati ne bayan halartar wani taro cikin dare ba tare da rakiyar jami’ann tsaro ba.
Direban Mista Aziegbemi, ya bayyana cewar ya lura wasu motoci na biye da su a baya tun da suka bar gidan gwamnati, amma bai taba tsammanin masu mugun nufi ba ne.
“Bayan wasu ‘yan mintina kaɗan sai na sauya hanya domin kubuce wa motar da ke biye da mu, amma sai ta sake biyo bayanmu ta tare mana hanya. Sai suka ce wa ubangidana ya shiga motarsu suka tafi da shi,” in ji shi.
Kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Edo, SP Chidi Nwabuzor ya tabbatar da faruwar lamarin.
Ya ce Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bai wa tawaga ta musamman umarnin bin sawun maharan domin ceto shugaban jam’iyyar.
Ita ma gwamnatin Jihar Edo, ta ce ta ƙara sanya ido tare da haɗa gwiwa da jami’an tsaro domin ganin an ceto shugaban jam’iyyar ta PDP.
Wata sanarwa da Kwamishinan yada labaran jihar, Chris Nehikhare ya fitar, ta ce gwamnatin jihar ta haɗa kai da jami’an tsaro domin ganin ya kubutar da shugaban jam’iyyar cikin koshin lafiya.