Maharan da suka je garkuwa da magidanci sun dauke matarsa
Maharan da suka je garkuwa da magidanci sun yi awon gaba da matarsa
Wasu da ba an san ko su waye ba sun sace wata mata mai suna Misis Chinagorom Frank da danta a yankin Etiti Asa, da ke Karamar Hukumar Ukwa ta Yamma a Jihar Abia, ‘yan mitoci kadan bayan sun fito daga gida.
Mazauna wurin da abun ya faru sun ce masu garkuwa da mutanen sun zo ne a kan babura suka yi awon gaba da matar da danta.
- Buratai ya soke taron shekara bayan soja ya kamu da COVID-19
- Badakalar fansho: Maina ya sake sumewa a kotu
- Rahama Sadau ce mace mafi tashe a Najeriya a 2020 —Google
Majiyarmu ta ce, maharan sun je ne da nufin yin garkuwa da mijin matar amma da ba su tarar da shi ba, sai suka dauki matar da dan suka tafi da su wurin da ba wanda ya sani.
Har yanzu dangin matar ba su da masaniyar inda aka tafi da su, saboda har zuwa lokacind da ake hada wannan rahoto ba a tuntube su don karbar kudin fansa ba.