Maharba sun kama mutum 4 da ake zargi da garkuwa da mutane a Taraba

Maharba sun kama wasu mutum hudu da ake zargi da satar mutane a Jihar Taraba.

Maharba sun kama mutum 4 da ake zargi da garkuwa da mutane a Taraba

Masu Garkuwa da Mutane

Maharba sun kama wasu mutum hudu da ake zargi da satar mutane a Jihar Taraba.

Shugaban kungiyar maharba a Jihar, Dantala Adamu, ya shaida wa Aminiya cewa sun kama mutunen hudu a wani tsauni da ke kan iyakar Kananan Hukumomin Bali da Ardo-Kola a daren Juma’a.

Ya ce wadanda suka kama din na cikin gungun ‘yan taaddan da suke sace jama’a a kauyuka da ke Kananan Hukumomin.

Ya ce wadanda suka kama sun bayyana cewa suna da hannu a cikin ayyukan ta’addanci tare da sace mutane .

Daya daga cikin wadanda aka kama mai suna Kwamanda, ya shaida wa wakilinmu cewa shi ne shugaba a cikin dabar masu sace mutane kuma yana da yara shida wadanda yake amfani da su wajen sace mutanen.

Kwamanda ya ce shi dan asalin Karamar Hukumar Ningi ne da ke Jihar Bauchi, kuma ya sace mutane da dama saannan ya karbi miliyoyin kudade daga hannun ‘yan uwansu.

Ya ce wani mutum daga anguwan Baba Yau a cikin garin Jalingo, babban birnin Jihar, wanda sya ce shi ne yake kawo masu bindigogi da albarusai.

Maharban dai sun mika wadanda suka kama a fadar Sarkin Jalingo domin kafa shaida kafin a mika su ga jami’an yansanda

Zaɓen Edo: Duk wanda ya kaɗa ƙuri’a ya koma gida ya zauna — ’Yan sanda

Hotunan yadda Zaɓen Gwamnan Edo ke gudana

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo