Maharba sun kashe ’yan bindiga 4 bayan Harin Cocin ECWA a Kogi
Hukumomi sun tabbatar cewa an kashe ’yan bindiga huɗu a yayin harin da suka kashe wani mutum 1, suka sace wasu 13 a wani Jihar Kogi.
Mafarauta
Hoto: ABC News
Hukumomi sun tabbatar cewa an kashe ’yan bindiga huɗu a yayin harin da suka kashe wani mutum 1, suka sace wasu 13 a wani Jihar Kogi.
A ranar Litinin da dare Gwamnatin Jihar Kogi ta sanar cewa mafarauta sun kashe ’yan ta’adda hudu a arangama, bayan ’yan bindiga sun kai hari a wani coci, inda suka kashe mai ibada guda ɗaya tare da yin garkuwa da wasu 13.
Kwamishinan Yada Labarai na jihar, Kingsley Fanwo, ya shaida wa manema labarai a Lokoja cewa mafarauta da ’yan banga sun yi musayar wuta da ’yan bindigar, inda suka kashe miyagu hudu, wasu da dama suka tsere da raunukan harbin bindiga.
A ranar Lahadi maharan suka kutsa cikin cocin ECWA da ke Aiyetoro-Kiri, Ƙaramar Hukumar Kabba/Bunu, a lokacin da ake gudanar da ibada.
Kwamishinan ya ƙara da cewa jami’an tsaro, ciki har da sojoji da ’yan sanda, sun isa yankin domin tabbatar da tsaro. “An taƙaita motsinsu ta hanyar tsarin tsaronmu. Muna da ƙwarin gwiwa cewa za a ceto mutanen da aka sace,” in ji Fanwo,
Ya bayyana cewa gwamnan jihar ya nemi tallafin Rundunar Sojin Saman Najeriya domin taimaka wa sojoji, ’yan sanda da mafarauta a aikin da suke yi a ƙasa.
Kwamishinan ya ce Hukumar Tsaron Sirri ta DSS tana bayar da bayanan leƙen asiri, yayin da mafarauta da ’yan banga ke ci gaba da bin sawun maharan a dazuka.
Jihar Kogi, wacce ke iyaka da jihohin Neja da Kwara, ta fuskanci ƙaruwar hare-haren ’yan ta’adda a ’yan watannin nan.
Fanwo ya ce gwamnati na ƙara ƙarfafa tsaro domin dakile barazanar, musamman hare-haren da ake kai wa “wuraren da ba su da kariya kamar coci-coci.”
Harin ya biyo bayan wani makamancinsa da aka kai makonni da suka gabata a Ejiba, inda ’yan bindiga suka sace masu ibada daga cocin Cherubim and Seraphim, ciki har da fasto da matarsa.
Har yanzu suna tsare da su bayan sun bukaci kudin fansa na naira miliyan 100.