Maharba sun koka kan hana farauta a Yobe

Maharba da masu sayar da namun daji a Jihar Yobe sun koka da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na haramta musu sana’o’insu ba tare da samar musu wata madafa ba. Shugaban maharba na karamar Hukumar Fune kuma jigo a kungiyar maharba ta jihar Malam Suleimanu Dingale ne ya bayyana wa Aminiya haka, bayan da […]

Maharba sun koka kan hana farauta a Yobe
Maharba sun koka kan hana farauta a Yobe

Maharba da masu sayar da namun daji a Jihar Yobe sun koka da matakin da gwamnatin jihar ta dauka na haramta musu sana’o’insu ba tare da samar musu wata madafa ba. Shugaban maharba na karamar Hukumar Fune kuma jigo a kungiyar maharba ta jihar Malam Suleimanu Dingale ne ya bayyana wa Aminiya haka, bayan da gwamnatin jihar ta haramta sayar da namun daji da yin farauta don dakile yaduwar cutar Ebola da ake danganta ta da wasu namun daji. Shugaba maharban ya ce ya shafe sama da shekara 40 yana gudanar da sana’ar ta harbo namun daji yana kawo wa kasuwanni don sayarwa, kuma a haka shi da sauran ’yan uwansa maharba ke rayuwa su da iyalansu. “Sai aka wayi gari wata cuta wai ita Ebola da ake alakanta ta da cin wasu namun daji, ta sa an yi kudin goro ga dukan namun daji gwamnatin Yobe ta haramta farauta ko sayar da namun daji, wanda hakan ya jefa su cikin matsala,” inji shi.  Ya roki gwamnatin jihar ta samar musu da abubuwan yi tunda dama can sun dogara ne da sana’ar don samar wa kansu madafa.