‘Maharbi da zomo’

Akwai wani maharbi wanda duk kauyensu babu wanda ya kai shi iya harbi. Rannan yunwa ta dame shi sai ya tafi farauta. Ya hada tarko ko zai samu naman daji ya yi sanwa. Can sai zomo ya fada tarkon maharbi. Zomo ya yi ta kokarin fita daga tarko amma ya gagara. A maimakon zomo ya […]

‘Maharbi da zomo’
‘Maharbi da zomo’

Akwai wani maharbi wanda duk kauyensu babu wanda ya kai shi iya harbi. Rannan yunwa ta dame shi sai ya tafi farauta. Ya hada tarko ko zai samu naman daji ya yi sanwa. Can sai zomo ya fada tarkon maharbi. Zomo ya yi ta kokarin fita daga tarko amma ya gagara. A maimakon zomo ya roki maharbi ya taimaka ya bar shi sai yace da maharbi “idan ka fitar da ni zan nuna maka inda sauranmu suke kuma za ka samu abin sanwa da yawa”. Jin haka, sai maharbi ya ce “ashe kai dan yaudara ne saboda haka sai na kashe ka”. Nan take maharbi ya yanka zomo ya yi sanwa da shi.
Da fatan Manyan Gobe zasu zama masu alkawari ba masu yaudara ba. Kuma za su dauki halayya nagari domin samun mafita a kodayaushe.