Mahari ya kashe uba da dansa a Kano
Wani maharin da ba a san ko wane ne ba ya fille kan wani mutum mai suna Malam Nuhu, wanda ke zaune a kauyen Tumfafi da ke Karamar Hukumar Garko ta Jihar Kano. Shaidu sun ce a baya wani maharin ya yi barazanar kashe Malam Nuhu a lokacin da ya je gidansa ya daba masa […]
Wani maharin da ba a san ko wane ne ba ya fille kan wani mutum mai suna Malam Nuhu, wanda ke zaune a kauyen Tumfafi da ke Karamar Hukumar Garko ta Jihar Kano.
Shaidu sun ce a baya wani maharin ya yi barazanar kashe Malam Nuhu a lokacin da ya je gidansa ya daba masa wuka a hannunsa.
- Dan Najeriya ne ya kirkiro rigakafin COVID-19 a Amurka
- Dattijo ya nemi budurwa ta biya biya shi N50,000 saboda kin auren shi
- Ta hallaka budurwar tsohon saurayinta ta kona gidansa
Rahotanni sun ce bayan ya fille kan Nuhu, sai maharin ya tsere zuwa inda ba a sani ba.
Jin haushin kisan da aka yi wa mahaifinsa, dan Malam Nuhu ya bi diddigin maharin, amma maharin ya fi karfinsa ya yi ta sarar shi har sai da ya yanke jiki ya fadi matacce.
Wani ganau ya bayyana cewa an riga an binne mamatan su biya a garin na Tumfafi cikin matukar tashin hankali.
Har zuwa lokacin hada wannan rahoton, ba a samu jin ta bakin Kakakin Rundunar ’Yan Sanda ta jihar, DSP Abdullahi Haruna ba.