Mahauci ya kashe abokinsa saboda Naira 100 a Jigawa

‘Yan sanda a jihar Jigawa sun gurfanar da wani mahauci dan shekara 30 mai suna Aminu Umar akan laifin kashe abokinsa saboda gardamar biyan kudi na Naira 100 akan fede fatar akuya a mahauta. Umar dan asalin garin Mijiyawa sun samu sabani tsakaninsa da abokin sana’arsa Sani Bala da ke zaune a rukunin gidaje na […]

Mahauci ya kashe abokinsa saboda Naira 100 a Jigawa

‘Yan sanda a jihar Jigawa sun gurfanar da wani mahauci dan shekara 30 mai suna Aminu Umar akan laifin kashe abokinsa saboda gardamar biyan kudi na Naira 100 akan fede fatar akuya a mahauta.

Umar dan asalin garin Mijiyawa sun samu sabani tsakaninsa da abokin sana’arsa Sani Bala da ke zaune a rukunin gidaje na unguwar Katutu a karamar Hukumar Ringim. Duk matasan ‘yan garin Ringim ne, Umar ya yi sanadin kashe abokin fadansa ne ta hanyar baiwa hammata iska.