Mahaukaci ya shekara 11 a keji

Wani mutum mai fama da tabin hankali a kasar Sin, iyayensa sun kulle shi a cikin keji bayan da ya yi wa wani yaro dukan tsiya har ya mutu, kamar yadda kafafen yada labarai suka bayyana, inda aka yi ta baza hotunansa a cikin kejin.Mutumin mai suna Wu Yuanhong, dan shekara  42, yana zaune ne […]

Mahaukaci ya shekara 11 a keji
Mahaukaci ya shekara 11 a keji

Wani mutum mai fama da tabin hankali a kasar Sin, iyayensa sun kulle shi a cikin keji bayan da ya yi wa wani yaro dukan tsiya har ya mutu, kamar yadda kafafen yada labarai suka bayyana, inda aka yi ta baza hotunansa a cikin kejin.
Mutumin mai suna Wu Yuanhong, dan shekara  42, yana zaune ne a kan wani bargo, inda aka daure shi da kaca, daga shi san dan kamfai da guntuwar riga.
An gano yana fama da mummunan tabin hankali, tun yana dan shekara 15, kuma a shekarar 2001 ya yi ta dukan wani karamin yaro dan shekara 13 har ya kashe shi, kamar yadda wata jarida da ke fitowa kullum ta bayar da labarinsa a shafin yanar sadarwarta.
Hukumomin shari’a na yankin Jiangdi sun sake shi daga kurkuku bayan zaman kaso na shekara daya, musamman saboda ganin cutar da yake fama da ita babu wata doka a kansa. Kuma babu wani bincike mai zaman kansa da aka gudanar da zai tantance musabbabin abin da ya aikata ba.
Bayan fitowar Wu daga kurkuku, an sanya masa sasari, amma mahaifiyarsa, mai suna Wang Mudiang, ta kera masa keji bayan da ya gudu, ya ika yawo a kwauyensu yana tsorata mutane. Kamar yadda rahotanni suka bayyana.
Iyayensa sun yi matukar kokawa a lokacin da suka jefa cikin keji, inda rahotanni suka yi nuni da cewa sai da ya sake gudu, don haka suka kera masa wani kejin mai karfin gaske, ta yadda suka samu damar turke shi a wuri guda.
“Ta yiwu dana mahaukaci, mai dukan mutum ya kashe shi, amma har yanzu dana ne. Da hannuna na saka shi cikin keji, wannan al’amari na damuna, tamkar na caka wa cikina wuka,” a cewar Wanga kamar yadda wata jarida ta ruwaito daga bakinta.
“duk sa’adda na kaimasa abinci, na kan tsaya a gaban kejin ina kuka,” injita, har ma ta c e: “Hawayena yanzu sun kafe.”
Wanga na ciyar da danta abinci sau uku a rana, sannan ta ajiye a kn masa tsumma, ta kuma samo masa kwanon da zai yi kashi ko fitsari a kai.
Haka ake kyale mahaukat aa kasar Sin su yi ta yawo ba tare da an nema musu magani ba, saboda rashin kudi da kwararrun likitocin kula da lafiya, musamman a yankunan akrkara.
Ma’aikatar lafiya ta kasar ta bayyana cewa a shekarar 2010, tana da likitocin tabin kwakwalwa dubu 20, a kasar da yawan al’ummarta ya kai biliyan daya da miliyan dari uku d arabi, a ruwar jaridar China daily.
Hukumomin kasar sun kiyasta cewa a shekarar 2009, akwai mutane kimanin miliyan 170 da ke fama da tabin hankali, inda a kalla mutum fiye da miliyan 16 ke hauka tuburan. Jaridar da ta ruwaito labarin, ta bayyana cewa jami’an hukuma, sun bayyana cewa suna taimaka wa iyayen Wu da man girki da shinkafa, inda suka bayyana cewa karamar Hukumar Jiangdi na bayar da dan tallafi ga iyalai matalauta wadanda ke da dan uwa da ke hauka tuburan.
Sai dai jami’an ’yan sanda da ke Nanyang, wadanda ke kula da daukacin Shangfan, sun ce ba su da masaniya kan wannan al’amari, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na AFP ya ruwaito.

An buƙaci mazauna Benuwe su yi ƙaura saboda fargabar ambaliyar ruwa

Abubuwan da ya kamata ku sani game da Zaɓen Edo

Ban zama Shugaban Kasa don na tara kuɗi ba — Tinubu

Babu buƙatar mu riƙa tsayar da motoci muna duba takardu — ’Yan sanda