Mahaukaci ya tarwatsa rumfar zabe a Umuahia

Wani matashin mahaukaci ya yi sanadiyyar dakatar da kada kuri’a a rumfar zabe ta Urban unit 1 da ke cocin Methodist a Umuahia babban birnin jihar Abiya. Lamarin ya faru ne lokacin da wani bakon mutum ya halarci harabar rumfar zaben ya fara ya dabi’u irin na mahaukaci. A  lokacin da jami’an tsaron rumfar zaben […]

Mahaukaci ya tarwatsa rumfar zabe a Umuahia

Wani matashin mahaukaci ya yi sanadiyyar dakatar da kada kuri’a a rumfar zabe ta Urban unit 1 da ke cocin Methodist a Umuahia babban birnin jihar Abiya.

Lamarin ya faru ne lokacin da wani bakon mutum ya halarci harabar rumfar zaben ya fara ya dabi’u irin na mahaukaci.

A  lokacin da jami’an tsaron rumfar zaben suka rike shi sai suka fara zargin mashayin tabar wiwi ne.

Akwatunan zabe sun lalace lokacin da matashin ya afka rumfar zaben.