Mahdi Shehu ya ba Jami’ar Jihar Kaduna motar kashe gobara

Ranar Juma’ar da ta gabata ne wani dan kasuwa da ke Kaduna, Alhaji Mahdi Shehu ya ba Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) motar kashe gobara. Idan ba a manta ba makonni biyu da suka wuce ne aka yi gobara a jami’ar inda ta kone tare da lalata dukiya mai yawa a sashin karantar da kwamfuta da […]

Mahdi Shehu ya ba Jami’ar Jihar Kaduna motar kashe gobara
Mahdi Shehu ya ba Jami’ar Jihar Kaduna motar kashe gobara

Ranar Juma’ar da ta gabata ne wani dan kasuwa da ke Kaduna, Alhaji Mahdi Shehu ya ba Jami’ar Jihar Kaduna (KASU) motar kashe gobara. Idan ba a manta ba makonni biyu da suka wuce ne aka yi gobara a jami’ar inda ta kone tare da lalata dukiya mai yawa a sashin karantar da kwamfuta da ke jami’ar.
Alhaji Mahdi Shehu ya ce ya kai taimakon motar ce domin tallafa wa jami’ar saboda abin da ya faru, inda ya ce ya lura a ranar da gobarar ta tashi a jami’ar motar kashe gobara ta kamfanin Mahdi Dialokue Group ce ta taimaka wajen kashe wutar domin jami’ar ba ta da motar kashe gobara.
Alhaji Mahdi Shehu ya ce, motar zai taimaka wajen magance asarar rayuka da dukiyar malamai da dalibai da sauran kadarorin jami’ar.
Da yake mika makullan motar, Alhaji Mahdi Shehu ya ce bai dace ba jami’a kamar KASU a ce ba ta da motar kashe gobara. “Mun bayar da motar ce domin taimaka wa jami’ar domin kauce wa abin da ya faru a kwanakin baya. Mun kuma yi haka ne domin ba da gudunmawarmu ga ci gaban jami’ar da ilimi. Muna kira ga sauran masu hannu da shuni su ziyarci jami’ar domin duba irin gudumawar da za su bayar don inganta jami’ar, musamman abubuwan da za su ciyar da ita gaba. Duk mutumin da ya san tarihin wannan jami’a a shekarun da suka gabata, ya ga yadda take a yanzu, zai tabbatar da cewa an yi amfani da ilimi da kwarewa wajen ingantata,” inji shi.
Alhaji Mahdi ya kuma bayyana cewa tallafin babu abin da ya hada shi da siyasa,“Ba na son siyasa, ba na yin ta, ba kuma zan yi ba,” inji shi.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Barnabas kurid ya nuna matukar farin cikinsa kan tallafin motar kuma ya ce za su yi amfani da ita ta hanyar da ta kamata.
Kwanakin baya ma kamfanin Alhaji Mahdi ta tallafa wa akalla yara dubu 10 da za su yi jarabawar shiga jami’a (JAMB) a Rigasa, Kaduna.