Mahmoon Baba-Ahmed: Dan jarida mai gaskiya da rashin tsoro ya kwanta dama
An ranar Alhamis din makon jiya ne Allah Ya yi rasuwa ga fitaccen dan jaridar nan kuma daya daga cikin marubuta a wannan jarida, Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed rasuwa, bayan ya yi jinya ta gajeren lokaci. Marigayi Mahmoon Baba-Ahmed har zuwa lokacin da Allah Ya karbi rayuwarsa yana aikin jarida tun daga yarintarsa. Kuma mako daya […]
An ranar Alhamis din makon jiya ne Allah Ya yi rasuwa ga fitaccen dan jaridar nan kuma daya daga cikin marubuta a wannan jarida, Alhaji Mahmoon Baba-Ahmed rasuwa, bayan ya yi jinya ta gajeren lokaci.
Marigayi Mahmoon Baba-Ahmed har zuwa lokacin da Allah Ya karbi rayuwarsa yana aikin jarida tun daga yarintarsa. Kuma mako daya kafin ya koma ga Allah ya yi rubutu wanda shi ne rubutunsa na karshe a Aminiya mai kanun: ‘Darasin haduwar Obasanjo da Buhari a Habasha.’
Wadanda suka yi aiki ko kuma hulda da marigayin sun bayyana shi da mutum mai sadaukar da kai da kwazo ga aiki, kuma mutum ne da aka shaide shi da tsantseni da gudun abin hannun mutane, ga kuma rungumar jama’a ba tare da lura da aji ko matsayin da suke kai ba.
daya daga cikin abokan fara aikinsa mai suna Abdullahi Nuhu, tsohon Ma’aikacin a Gidan Rediyon Jihar Arewa (BCNN) ya bayyana cewa, “Muna tare da marigayi tun kafin mu yi aure duk da ya girme ni dan kadan, har zuwa lokacin da muka mallaki hankalinmu, kuma har Allah Ya sa muka fara aikin jarida kusan tare a 1971 a BCNN. Ni ina bangaren talabijin shi kuma yana bangaren rediyo. Kuma marigayin a harkar aikin jarida ba ya da tsoro ko kadan, ba ya da kwadayi, kuma duk zaman da kuke yi da marigayi ba zai fadi abin da ba ka fada ba, domin kawai ba ka shiri da shi, kuma ba zai hana ya fada abin da ka yi na alheri ba. Shi kusan kullum a cikin fadin gaskiyar abin da ka yi ne ba tare da tsoro ko gudun wani abu ya same shi ba.”
Ya kara da cewa “Don haka ne ya yi fice a kan aikin wasta labarai, kuma har kusan karshen rayuwarsa yana ba da gudunmawa a kafafen watsa labarai da dama. Hakika mun yi rashi ma’aikaci mai kishin aikin jarida. Allah Ya gafarta masa, amin.” Marigayi Mahmoon ya rasu ne a gidansa da ke Kaduna misalin karfe 11 na dare a ranar Alhamis yana da shekara 74. Kuma an yi jana’izarsa a Masallacin Sultan Bello da ke Kaduna washegari bayan idar da Sallar Juma’a. dan uwan marigayi, kuma mai bi masa Dokta Hakeem Baba Ahmed, Shugaban Ma’aikata a Ofishin Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Bukola Saraki cewa ya yi, “Mu zuriyar Baba Ahmed mun yi rashi babba, kasancewar Mahmoon a gidanmu shi ne babba a maza don haka ya zama tamkar uba ne a wurinmu domin ya yi amfani da tarbiyyar da mahaifinmu ya yi mana na cewa duk abin da zai yi ya ji tsoron Allah ya yi shi da gaskiya, ya kuma tsaya wa gaskiya, kuma ya yi abin da yake ganin ya fi karbuwa a wurin jama’a, wato abin da mutane suke so idan abin na gaskiya ne. To abin da aka san shi da shi ke nan a aikin jarida da aikin gwamnati da sauransu, a kan wannan akidar ya tsaya da kuma tarbiyar iyaye da kuma bin umarnin Allah Subahanahu Wata’ala don haka, alhamdulillahi yau ga shi abin da ya bari a baya shi ne ayyukansa na alheri, kuma ya bar zuriya da yawa domin ba ’ya’yan da ya haifa kawai ya bari ba, ya tafi duk ya bar mu.”
Dokta Hakeem ya kara da cewa, “dan uwana marigayi Mahmoon ya fara jinya a tsaitsaye kamar wata uku da suka wuce, amma kuma ciwon bai hana shi yin abin da zai iya yi ba, domin duk ranar da ya samu sauki yakan fito ya yi aikin da ya saba, saboda haka har Allah Ya dauki ransa bai bar rubuce-rubucen da yake yi muku ba. Domin a makon jiya na yi masa waya da daddare domin mu gaisa, sai ya ce min ya samu sauki ga shi nan yana yi wa jaridar Aminiya rubutu a filinsa na MATASHIYA da yake yi duk mako. Har nake ce masa wai har yanzu ba za ka huta ka daina rubutun nan ba, sai ya yi dariya. Ka ji yadda mukayi da shi,” inji Dokta Hakeem.
Mahmoon ya yi aikin jarida a wurare da dama, ya fara aiki a 1971 da BCNN, sannan ya taba yi aiki a kamfanin buga jaridan New Nigerian da Gaskiya Ta Fi Kwabo matsayin karamin Editan, daga nan ya yi wakilin Rediyon BCNN wanda ya koma FRCN na Kaduna a jihohin Bauchi da Kano da Borno da Filato da kuma Legas. Kuma a 1983 marigayi Gwamnan Jihar Kano Alhaji Sabo Bakin Zuwo ya nada shi Janar Manajan Gidan Rediyon Jihar Kano, kafin ya sake dawowa gidan Rediyon Najeriya na Kaduna.
daruruwan jama’a sun yi ta tururuwa zuwa ta’aziyyar marigayin ga danginsa. cikin wadanda suka je ta’aziyyar har da tsofaffin gwamnonin Jihar Kaduna Alhaji Abdulkadir Balarabe Musa da Alhaji Mukhtar Lamaran Yero da tsofaffin ministoci, Alhaji Umaru Dembo da Dokta Aliyu Modibo da Sanata Bala Ibn Na’Allah da wakilan Mai martaba Sarkin Zazzau Alhaji Shehu Idris, yayin da Mataimakin Babban Editan Kamfanin Media Trust Limited mai buga jaridun Daily Trust da Aminiya, Malam suna Mahmud Jega da wakilanmu da ke Zariya suka wakilci kamfanin wajen mika ta’aziyyarsu.
Masu ta’azziyar sun bayyana cewa an yi rashin dan kishin kasa kuma kwararren dan jarida mai fadin gaskiya ba tare da tsoro ba.
Marigayi Mahmoon Baba-Ahmed ya rasu ya bar mace daya da ’ya’ya takwas da jikoki shida. Allah Ya jikansa da rahama.