Mahara sun yi garkuwa da jami’in tsaro da matarsa

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani hafsan Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) da matarsa bayan sun kashe ’yar uwarsa a daren Talata. Maharan sun yi ta harbi a lokacin da suka mamaye gidan jami’in wanda dan uwa ne ga tsohon Ministan Yada Labarai Labaran Maku, a yankin Gudu da ke Karamar Hukumar […]

Mahara sun yi garkuwa da jami’in tsaro da matarsa

’Yan bindiga sun yi garkuwa da wani hafsan Hukumar Shige da Fice ta Najeriya (NIS) da matarsa bayan sun kashe ’yar uwarsa a daren Talata.

Maharan sun yi ta harbi a lokacin da suka mamaye gidan jami’in wanda dan uwa ne ga tsohon Ministan Yada Labarai Labaran Maku, a yankin Gudu da ke Karamar Hukumar Akwanga a Jihar Nasarawa.

Kwaturolar NIS ta jihar Zainab Lawal ta ce, “An yi garkuwa da Sufritenda Salisu Usman da matarsa aka kuma harbe ’yar uwarsa”.

Wani mazaunin Gudu ya ce ’yan bindigar sun harbe mutum daya domin su razana matasan unguwar da suka kawo musu turjiya.

Jihar Nasarawa mai makwabtaka da birnin tarayya Abuja na yawan fama da matsalar masu garkuwa da mutane.

Ko a ’yan makonnin da suka wuce wasu ’yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum 20 suka kuma kashe ’yan banga biyu a jihar