Mahukunta na bincike kan kashe ’yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu

Ɗaya daga cikin ’yan Najeriyar ya mutu ne bayan wata taƙaddama da ta shiga tsakaninsa da jami’an ’yan sanda.

Mahukunta na bincike kan kashe ’yan Najeriya biyu a Afirka ta Kudu

Hukumar Sa Ido kan Ayyukan ’Yan sanda ta Afirka ta Kudu (IPID) ta tabbatar da cewa tana binciken wani ƙorafi da aka shigar kan jami’an ’yan sanda a birnin Pretoria bayan mutuwar wasu ’yan Najeriya.

Hukumar ta ce an shigar da ƙorafin ne a makon da ya gabata, amma ba za ta iya fitar da cikakkun bayanai kan lamarin ba a wannan lokaci, saboda bincike na ci gaba da gudana.

Rahotanni sun nuna cewa ɗaya daga cikin ’yan Najeriyar ya mutu ne bayan wata taƙaddama da ta shiga tsakaninsa da jami’an ’yan sanda.

Haka kuma, a ranar 28 ga Yuni a lardin Mpumalanga, ’yan sanda sun tabbatar da cewa suna binciken kisan wani ɗan Najeriya, mai sana’ar gyaran gashi, wanda aka harbe a wajen shagonsa da ke garin eMalahleni, tsohon Witbank.

A cewar ’yansandan, wani mutum ɗauke da makami ne ya tare shi sannan ya harbe shi har lahira kafin ya tsere a cikin wata farar mota.

Har yanzu ba a kama kowa ba, kuma ba a bayyana dalilin kisan ɗan Najeriyar ba.

’Yan sandan sun yi kira ga duk wanda ke da bayanin da zai taimaka wajen cafke wanda ake zargi da aikata laifin da ya tuntuɓe su.