Mahukunta na neman jefa rayuwar Murja cikin hatsari —Lauya
Lauyan ya koka kan yadda ake neman jefa rayuwar Murja cikin hatsari.
Lauyan fitacciyar ’yar TikTok, Murja Ibrahim Kunya, Barista A. U. Haji, ya ce mahukunta na neman jefa rayuwar wadda yake karewa cikin hatsari.
Lauyan ya bayyana haka ne a ranar Litinin, yayin zantawa da manema labarai, bayan da aka kai Murja Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase don yi mata gwaji.
- ’Yan sanda sun ceto mutum 40, sun cafke mahara 10 a Taraba
- Gobara ta kone shaguna 50 a kasuwar ’yan Katako a Kano
“Mun samu labari daga tushe mai karfi cewar ga Murja an tafi da ita asibitin Dawanau, kuma ba mu yi kasa a gwiwa ba muka garzaya muka kama hanya kafin mu karasa sai aka kira mu cewa an fito da ita za a kai ta asibitin Nassarawa.
“Bayan sun kawo ta asibitin ba su bar mu mun gan ta ba, suka ce mana suna zuwa za su shiga su yi wani uziri.
“Ba mu damu ba, muka hadu da kanin mahaifiyarta wanda ya bayyana yadda aka yi tataɓurza da ita kan dole sai an yi mata allura a asibitin Dawanau, amma ta ki yarda.
“Wanda take nema za ta aura ta shaƙe wuyansa ta ce dole sai dai idan tare za a yi musu a dauki rayuwarsu,” in ji shi.
Lauyan ya koka cewar mahukunta na amfani da umarnin kotu wajen cin zarafi da danne hakkin wadda yake karewa.
A cewarsa babu inda doka ta hana a sanar da mutum halin da yake ciki game da lafiyarsa.
“A wannan yanayin da ake ciki matakin da hukumar da ke kula da asibitoci ta Jihar Kano ta dauka kuskure ne, domin rayuwar wadda muke karewa tana cikin hatsari.
“Kowace irin tuhuma ake yi mata, kotu abin da ta ce shi ne a je a duba lafiyarta, ba wai a fara ba ta magani ba.
“Ko mene ne ita da ’yan uwanta da lauyoyinta suna da hakkin samun rahoto kan mene ne bincike ya nuna kan abin da yake damun ta.”
Idan ba a manta ba a makon da ya gabata ne kotun shari’ar Muslunci da ke zamanta a unguwar PRP a Jihar Kano, ta bayar da umarnin yi wa Murja gwajin ƙwaƙwalwa.
Hukumar Hisbah a jihar ce ta kama matashiyar tare da gurfanar da ita a gaban kotun, kan zargin koyar da karuwanci da bata tarbiyyar kananan yara.