Mai aikin gawayi ya kashe dan sanda a kan Naira dubu 120
Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta yi nasarar kama wani mutum mai kimanin shekara 30 da ake zargi da kashe dan sanda mai mukamin kofur wanda ke aiki a yankin na Odeda na jihar. Marigayin dan sandan mai suna Gbenga Adeyejo ya kulla alakar kasuwancin gawayi ne da wanda ake zargi da hallaka shi, wanda […]
Rundunar ’Yan sandan Jihar Ogun ta yi nasarar kama wani mutum mai kimanin shekara 30 da ake zargi da kashe dan sanda mai mukamin kofur wanda ke aiki a yankin na Odeda na jihar.
Marigayin dan sandan mai suna Gbenga Adeyejo ya kulla alakar kasuwancin gawayi ne da wanda ake zargi da hallaka shi, wanda shine shugaban ’yan kabilar Tibi da ke zaune a yankin Opeji wani kauye mai nisa daga Karamar Hukumar Odeda, inda mazauna yankin ke sana’ar yin gawayi.
Lokacin da yake yi wa ’yan jarida karin haske a dajin da lamarin ya auku, Kwamishinan ’Yan sandan Jihar Ogun, Ahmad Iliyasu ya ce sun kama wanda ake zargin ne bayan karar da mahaifin mamacin ya shigar ga ’yan sanda, inda ya shaida musu cewa a ranar 24 ga watan Nuwamban da ya gabata dansa ya ziyarce shi a gidansa a garin Ilorin, Jihar Kwara, inda ya ba shi labarin kasuwancin gawayin da ya kulla da wani shugaban al’ummar Tibi.
Ya ce a lokacin da dansa ke yi masa wannan bayani shugaban al’ummar Tibin ya kira shi ta waya, ya shaida masa cewa ya kammala hada masa gawayin don haka ya zo ya karba, ganin haka ne dan ya bar Ilorin ya koma Jihar Ogun. Ya ce bayan da dansa ya isa gidan mutumin ya buga masa waya ya shaida masa cewa yana gidan, tun daga nan bai sake jin duriyarsa ba, lamarin da ya dimauta shi ya garzayo zuwa Ogun domin ya bi bahasi.
“Bayan da ya shigar da kara ne a ofishin ’yan sandan yankin da lamarin ya auku, inda a nan ne marigayin ke aiki, nan take DPO na yankin Babban Sufirtanda Baba Muhammed ya tsunduma cikin aiki, inda ya yi nasarar kama wanda ake zargin mai suna Jonathan Tsekar, Shugaban Al’ummar Tibi na Opeji, baya ga shi kuma mun kama karin mutum biyu da suka yi huldar karshe da mamacin, mun yi amfani da hanyoyin bincike na kimiyya wajen kama wadanda ake zargin, kuma zamu tabbatar an hukunta su kamar yadda doka ta tanada da zarar mun kammala bincike,” inji Kwamishinan ’Yan sandan.
Wanda ake zargi Jonathan Tsekar ya shaida wa manema labarai cewa ba da gangan ya kashe dan sandan ba, ya ce marigayin ya ba shi Naira dubu 120 don ya yi masa gawayi, sai dai a lokacin da ya zo ya duba aikin da ya sa shi ya yi masa, sai ya tarar bai yi aikin ba, hakan ne ya sanya dan sandan ya fusata, “Ganin ya hasala ne ni kuma na tsorata da matakin da zai iya dauka sai na dauki sanda na buga masa a kansa, sai da na jira zuwa wani lokaci da na tabbatar ba ya motsi sannan na binne shi. Na yi nadama, ba nufina in kashe shi ba,” inji wanda ake zargin.
Kwamishina Ahmad Iliyasu ya yi kira ga jama’a su rika taka-tsantsan da mutanen da suke hulda da su, “Ka san ba a rubutawa a goshin mutum cewa mutumin kirki ne ko akasin haka,” inji shi.