Mai aikin shara ya mayar da Dala 10,000 da ya tsinta a Kano
Cikin farin ciki Balaraben bai san lokacin da ya rungume mai aikin sharan ba
Wani matsahi mai aikin shara ya mayar da Dala 10,000, kimanin Naira miliyan 16, da ya tsinta a Filin Jirgi na Malam Aminu da ke Kano.
Matashin mai suna Auwal Ahmed Dankode, mai aikin sharan jirgin sama ne, kuma ya tsinci kuɗaɗen ne a cikin jirgin kamfanin EgyptAir, ranar Laraba da misalin karfe 1.30 na rana.
Nan take Auwal, wanda ɗan asalin ƙauyen Dankode ne da ke Ƙaramar Hukumar Bunkure a Jihar Kano, ya sanar da mahukunta ya kuma damka wa manajan jirgin kuɗaɗen tsintuwar.
- NAJERIYA A YAU: Yadda Ambaliya Ke Raba Dubban ‘Yan Najeriya Da Muhallansu
- Mutane 179 sun mutu wasu 208,655 sun yi ƙaura saboda ambaliya —NEMA
Daga bisani wani bawan Allah Balarabe ya zao yana cibiyar kuɗaɗensa da suka bace, inda manajan kamfanin ya yi masa tambayoyi.
A karshe bisa bisa bayanan da balaraben ya yi aka tabbatar cewa kudaden nasa ne, sai manajan ya damƙa masa su, ya shaida masa abin da ya faru.
Cikin godiya da farin ciki Balarabe bai san sadda ya rungume mai sharan jirgin ba.
Dankode ya ce, “Mutane da yawa a filin jirgin sun daga ni sama suna yaba min bisa abin da nayi.
“Na ji dadi sosai kuma ina farin ciki. Ina godiya ga Allah da Ya ba ni damar farantawa wani.
“Ina yin aikina ne lokacin da na tsinci kudin. Na san nan take cewa ya kamata na sanar. Wannan ne abin da ya dace a yi,” in ji Auwal.