Mai aikin shara ya mayar da N40m da ya tsinta a Kano

Wani mai aikin shara ya mayar kudi kimanin Naira miliya 40 da ya tsinta ga mai su a Asibitin Abubakar Imam da ke unguwar Fagge a Kano

Mai aikin shara ya mayar da N40m da ya tsinta a Kano

Wani mai aikin sharar asibiti a Kano ya mayar da kudin da ya tsinta kimanin Naira miliya 40 ga mai su.

Malam Aminu Umar Kokar Mazugal ya tsinci kudin ne a dalolin Amurka a cikin wata jaka da mai su ya manta a Asibitin Abubakar Imam da ke unguwar Fagge.

Malam Aminu wanda matsakaicin ma’aikaci ne ya tsinci kudin a cikin wata jaka kuma ya mayar da kudin ga mai su, Alhaji Ahmed Abubakar, wanda ya manta da su a lokacin da ya je dubiyar mara lafiya a asibitin.

Alhaji Ahmed ya manta da kudin ne a wurin da ya dan zauna na dan lokaci a wurin ajiye motoci da ke kusa da masallaci, inda daga bisani ya wuce domin shiga jirgin sama.

Malam Aminu ya shaida wa wakilinmu cewa jim kadan da tafiyarsa mutumin ne shi kuma ya tsinci kudin a lokacin da yake aikin shara.

Ya ce daga bisani, bayan kimanin awa guda, mai kudin ya dawo yana cikiya, shi kuma ya mayar masa kayansa.

Shugaban Asibitin, Dokta Aminu Imam Yola, ya tabbatar da faruwar lamarin yana mai cewa hukumar gudanarwar asibitin ta sanar da Ma’aikatar Kula da Asibitoci ta Jihar Kano domin a karrama Malam Aminu.

Mun fara binciken turmutsutsin tallafin abinci — Shugaban ’Yan Sanda

Tinubu ya soke ayyukansa saboda rasuwar mutane a Abuja da Anambra

NNPC ya rage farashin fetur zuwa N899

Mutum 10 sun mutu a wajen rabon tallafin abinci a Abuja