Mai ba Gwamnan Bauchi Shawara zai fito takarar dan Majalisar Tarayya a Kebbi

Mai ba Gwamnan Jihar Bauchi Shawara a kan yin ayyuka bisa ka’ida Alhaji Mohammed Surajo Garba ya bayyana niyyarsa ta fitowa takarar dan Majalisar Tarayya daga Jihar Kebbi. Alhaji Mohammed Surajo Garba wanda yake shirin fitowa takarar don wakiltar kananan hukumomin Suru da Bagudo a karkashin Jam’iyyar PDP ya ce, ya fito takarar ce domin […]

Mai ba Gwamnan Bauchi Shawara zai fito takarar dan Majalisar Tarayya a Kebbi
Mai ba Gwamnan Bauchi Shawara zai fito takarar dan Majalisar Tarayya a Kebbi

Mai ba Gwamnan Jihar Bauchi Shawara a kan yin ayyuka bisa ka’ida Alhaji Mohammed Surajo Garba ya bayyana niyyarsa ta fitowa takarar dan Majalisar Tarayya daga Jihar Kebbi.

Alhaji Mohammed Surajo Garba wanda yake shirin fitowa takarar don wakiltar kananan hukumomin Suru da Bagudo a karkashin Jam’iyyar PDP ya ce, ya fito takarar ce domin kawo canji mai ma’ana a kananan hukumomin.
Alhaji Surajo Garba ya bayyana haka ne a lokacin da jama’ar kananan hukumomin Suru da Bagudo suka shirya masa gangamin nuna goyon baya domin ya wakilce su a Majalisar Tarayya.
Ya ce idan al’ummar mazabar suka zabe shi, zai jawo ayyukan ci gaba ga kananan hukumomin fiye da wanda yake wakiltarsu tun 1999, ba tare da tsinana musu abin a zo a gani ba.
dan takarar ya ce ya tabbatar wa matasan yankin cewa da zarar Allah Ya kai shi bisa wannan kujera zai kara taimaka musu da ayyukan yi da kuma sana’o’in hannu fiye da yadda yake taimaka masu a yanzu.
Ya kuma bukaci ’yan siyasa su nisanci mayar da siyasa tamkar wani kamfani na zuba jari ba, maimakon haka su rika sanya tsoron Allah cikin lamarinsu don lahirarsu ta yi kyau.