Mai bai wa budurwarsa motar alfarma ta sata ya shiga hannu a Kuwait

’Yan sanda sun kama mutumin da ke sato wa budurwarsa motar alfarma kowane wata a kasar Kuwait. Mai lafin ya shiga hannun jami’an ’yan sanda ne bayan da aka kama budurwarsa tana yawo a cikin wata motar alfarma da aka kai rahoton satar ta a yankin Al Ahmadi. Da jami’an ’yan sandman suka tambayi wannan […]

Mai bai wa budurwarsa motar alfarma ta sata ya shiga hannu a Kuwait
Mai bai wa budurwarsa motar alfarma ta sata ya shiga hannu a Kuwait

’Yan sanda sun kama mutumin da ke sato wa budurwarsa motar alfarma kowane wata a kasar Kuwait. Mai lafin ya shiga hannun jami’an ’yan sanda ne bayan da aka kama budurwarsa tana yawo a cikin wata motar alfarma da aka kai rahoton satar ta a yankin Al Ahmadi.

Da jami’an ’yan sandman suka tambayi wannan mata a inda ta samu wannan mota, sai ta bayyana musu cerwa kyauta ce daga saurayinta, inda ta yi karin haske da cewa a kowane wata sai ya ba ta kyauta mota,don kara dankon soyayyarsu.
Sai dai wannan budurwa ta yi matukar dimaucewa da ’yan sanda suka bayyana mata cewa motar da take tukawa ta sata ce.
Sai ta bayar da cikakkun bayanai game da saurayinta, har aka samu aka kama shi. Ya kuma amsa laifukan da ake tuhumarsa da su a lokacin da aka gudanar da bincike.
Ya ce, ya yi haka ne don budurwarsa ta yarda cewa, shi hamshakin attajiri ne, saboda haka ya rika sato motocin alfarma don biyan bukatun kashin kanta, kamar yadda jaridar Al-Watan ta ruwaito.
Ya ce, dabarar da yake yi wajen satar, ita ce ya yi kokarin sato mabudin motar daga akwatunan da masu motocin ke yin ajiya, sai kuma ya tafi da motocin don ya bai wa budurwarsa kyauta.