Mai buga kuɗin jabu ya shiga hannu a Ogun

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta yi nasarar kame wani mutum da ake zargi da zamba cikin aminci da tu’ammali da kuɗaɗen bogi. Mutumin mai suna Bidemi Idowu ɗan kimanin shekaru 41, wanda boka ne da ke aikin tsibbu ya shiga komar ’yan sanda ne bayan da ya karɓi Naira dubu 400 a wajan […]

Mai buga kuɗin jabu ya shiga hannu a Ogun

Rundunar ’yan sanda a Jihar Ogun ta yi nasarar kame wani mutum da ake zargi da zamba cikin aminci da tu’ammali da kuɗaɗen bogi.

Mutumin mai suna Bidemi Idowu ɗan kimanin shekaru 41, wanda boka ne da ke aikin tsibbu ya shiga komar ’yan sanda ne bayan da ya karɓi Naira dubu 400 a wajan wani matashi ɗan shekara 21 da nufin zai yi masa maganin kuɗi, inda zai ninka masa dubu 400 zuwa adadi mai yawa.

Bayan da bokan ya ƙarɓi kuɗin a hannun matashin sai ya ba shi wani magani ya ce ya je ya sha, bayan ya sha ne cikinsa ya kulle, ya yi ta murɗawa. Hakan ya sa ya ankarar da mahaifinsa, wanda ya shigar da ƙara zuwa ofishin ’yan sanda.

A cewar kakakin rundunar ’yan sandan Jihar Ogun, ASP Abimbol Oyeyemi bayan da rundunar ta sami takardar ikon yin binciken gidan wanda ake zargin, ta iske Naira dubu 400 da ya karɓa a wajan matashin kana an gano kuɗin jabu na kasashen ƙetare, waɗanda suka haɗa da Sefa dubu 59 da Dalar Amurka 50 guda 600 da kuɗin Najeriya na bogi ’yan Naira dubu-dubu

Tuni dai Kwamishinan ’yan sanda a jihar, Ahmad Iliyasu ya ba da umarnin iza ƙeyar wanda ake zargi don ya fuskanci shari’a.