Mai ciyar da iyalansa 9 da Naira 900 ya samu sauyin rayuwa cikin mako 2
Na fitar da zakkar fid-da-kai a karon farko a rayuwata — Malam Isa
Labarin Malam Hassan Isa, mai yankan farce, labari ne mai ratsa zuciyar ɗan Adam, wanda hakan ya taɓa zuciyar wasu suka kai masa ɗauki inda ya samu sauyin rayuwa a ƙasa da mako uku.
Labarinsa da aka buga a jaridar Aminiya ta ranar 5 ga Afrilun da ya gabata, ya nuna irin gwagwarmayar da yake yi, inda duk da irin ƙoƙarin da yake yi, da ƙyar yake iya samun Naira 900 don ciyar da iyalansa mai mutum tara.
- Alaƙar soyayya tsakanin jinsi ɗaya ta haramta a Iraqi
- Mahukunta sun gargaɗi Kanawa kan yaɗuwar cututtuka saboda tsananin zafi
Bayan labarin na Aminiya, rayuwar Malam Hassan ta canja, inda a ranar Asabar ta gabata da Aminiya ta sake ziyartar iyalan, ta gane wa idonta yadda rayuwar iyalan ta fara canjawa.
Malam Hassan Isa ya ce bayan buga labarinsa, ya samu tallafin mutane masu karamci da masu hannu da shuni daga jihohi daban-daban.
Waɗannan masu ba da tallafi sun ba da gudummawar jimillar Naira dubu 150, wanda hakan ya yi tasiri matuƙa wajen sauya halin da iyalinsa suke ciki.
Wani mai taimako da ba a bayyana sunansa ba, ya ba matarsa kyautar injin niƙa, kuma ya yi alƙawarin samar musu da kuɗi don fara sana’ar kiwon kaji, ta yadda za su samu sauƙin rayuwa.
Malam Hassan ya nuna jin daɗinsa da wannan tallafi da aka ba shi, inda ya ce Naira dubu100 ta farko da ya samu har ya gagara barci.
Ya ce, “Na ji kamar mafarki ne, na yi ta farkawa bayan mintuna kaɗan da yin barci don kawai in duba wayata don ganin ko da gaske ne kuɗin.”
Irin alherin da aka yi wa Malam Hassan da iyalansa na nuna ƙarfin tausayi da jin ƙai na al’ummar Nijeriya.
Har ila yau, ya nuna muhimmancin ba da labarun ɗaiɗaikun mutane da ke fuskantar matsala, domin hakan na iya zaburar da wasu su ɗauki matakin kai ɗauki.
Idan ba a manta ba, Aminiya ta ruwaito Malam Hassan yana cewa bai taba riƙe Naira 20,000 tasa ba.
Sai dai kuma bayan buga labarin, sai ga shi ya samu Naira dubu 150, sakamakon karamcin wata gidauniya da ta aiko da Naira dubu 100.
Ya kuma samu tallafin daga wasu mutane da suka haɗa da Naira 10,000, 17,000, 5,000, 3,000, 2,000, 4,000 da kuma Naira 9,000.
Malam Hassan ya miƙa godiyarsa ga duk wanda ya ba da gudunmawar da kuma ba shi damar samun kuɗin.
Ya yi yabo na musamman kan gudunmawar da wani ɗan jarida Mubarak Aliyu ya bayar, wajen tattara kuɗin daga dandalinsa na sada zumunta bayan ya bayyana labarin Malam Hassan a shafinsa na Facebook.
Bugu da ƙari, Malam Hassan ya bayyana cewa, sakamakon tallafin da iyalansa suka samu sun samu kayan abinci da man girki da kayan marmari da za su iya ci gaba da ci har na tsawon wata uku ba tare da sayen kayan abinci ba.
Ya bayyana godiyarsa ga duk wanda ya ba da gudunmawa, ya kuma yi addu’ar Baya ga kayan abinci da mabiya ƙarin yalwar arziki. Hakan yana nuna Allah Ya saka musu da alheri.
Mubarak suka samar ta Facebook, matarsa Malama Bilkisu ta samu kyautar injin niƙa, wanda wani daga Abuja ya tura mata.
Wannan mai taimakon ba wai kawai ya samar da injin niƙa ba ne, har ma ya yi alƙawarin aika kuɗi don taimaka wa Malam Hassan ya fara sana’ar kiwon kaji, in ji Mubarak.
Malam Hassan ya nuna jin daɗinsa ga wanda ya bayar da gudunmawar da duk wanda ya ba da gudunmawa wajen kyautata rayuwar iyalinsa.
Ya ce ko da mai ba da gudunmawar bai aika da kuɗi don kasuwanci ba, yana godiya kan canje-canje masu kyau da ya samu.
Na fitar da zakkar fid-da-kai a karon farko a rayuwata — Malam Isa
A karon farko a rayuwarsa Malam Hassan ya ce ya samu damar bayar da zakkar fid-da-kai wanda ake so duk Musulmin da ya mallaki abincin wuni ya yi a ƙarshen watan Ramadan.
Wannan sadaka na nufin sauƙaƙa wa Musulmi su yi Ƙaramar Sallah, cikin farin ciki don kawo ƙarshen azumin watan Ramadan.
Ya ce ya kuma fitar da zakkar ga iyalansa tara, inda ya ce ya samu natsuwa da farin cikin kasancewarsa cikin waɗanda suka samu damar shiga wannan sadaka.
“Na ji daɗin kasancewa cikin Musulmin da suka fitar da zakkar fid-da- kai a bana, a koyaushe ni ne nake karɓar sadaka duk shekara, amma ina godiya ga Allah Madaukakin Sarki da Ya ba ni damar bayar da ita bana,” in ji shi.
Karfinsa na bayar da zakkar ya nuna irin canjin rayuwa da ya samu da karin yalwar arziki. Hakan ya nuna muhimmancin mayar da hankali ga al’umma, musamman ga waɗanda ba su da wadata.
Matarsa Balkisa ta nuna farin cikinta tare da sanya albarka ga duk waɗanda suka ba su tallafi tare da cewa “Allah Ya rubuta a mizani”
Labarin Malam Hassan ya zama abin zaburarwa ga sauran mutane, inda yake kwaɗaitar da su wajen nuna karamci da jin ƙai ga mabuƙata da kuma himma wajen samar da kwanciyar hankali ta hanyar kyautatawa da sadaka.
Ingantuwar tattalin arziki ya yi tasiri mai kyau ga rayuwar iyalinsa, domin ya iya biya wa ’ya’yansa haƙƙoƙinsu na kuɗin PTA tare da saya musu sababbin riguna.
Hakan dai ya ba ’yan uwa farin ciki sosai, kasancewar rigar da suka saba yi a baya ta yage sun kuma kasa samun sababbi.
Malam Hassan ya nuna godiyarsa ga Allah da kuma jaridun Daily Trust da Aminiya da suka kawo masa agaji ta hanyar yin rahoto a kan rayuwarsa, wanda labarin ne ya yi sanadin canja rayuwarsa.
Ya kuma bayyana cewa yana da niyyar shigar da ƙaramin ɗansa makaranta nan ba da jimawa ba.