Mai Coronavirus ya sa kayan matarsa ya shiga jirgin sama

Ya sayi tikitin jirgin ne da sunan matarsa.

Mai Coronavirus ya sa kayan matarsa ya shiga jirgin sama

Mutumin da ya yi amfani da jabun takardu tare da shigar matarsa a filin jirgin
sama na Sultan Babullah da ke Ternate, kasar Indonusiya

Wani dan kasar Indonusiya da yake dauke da cutar Coronavirus ya shiga jirgin sama bayan da ya yi shigar matarsa sanye da nikabi kuma dauke da takardar shaida ta karya, sai dai asirinsa ya tonu nan take.

Kamfani Dillancin Labarai na AP ya ruwaito cewa, ’yan sanda sun ce wani ma’aikacin jirgin na Kamfanin Citilink da ya tashi daga Jakarta zuwa garin Ternate a Arewacin Lardin Maluku a ranar Lahadin makon jiya ce ya lura da lokacin da mutumin ya canja tufafinsa a bayin cikin jirgin.

“Ya sayi tikitin jirgin ne da sunan matarsa kuma ya gabatar da takardar shaidarsa da ta sakamakon gwajin Coronavirus da kuma ta allurar riga-kafi dauke da sunan matarsa.

“Dukkan takardun suna dauke da sunan matarsa,” inji Shugaban ’Yan sandan Ternate, Mista Aditya Laksimada bayan kama mutumin lokacin da ya sauka daga jirgin.

’Yan sanda sun dauke shi zuwa wajen yi masa gwajin cutar Coronavirus, inda sakamako ya nuna yana dauke da cutar.

Yanzu haka mutumin ya killace kansa a gida kuma ’yan sanda sun ce za su ci gaba da gudanar da bincike.

Kasar Indonusiya ta fi kowace kasa a yankin Asiya fama da cutar Coronavirus, inda aka samu sababbin kamuwa da cutar dubu 33 da 772, yayin da mutum 1,383 suka rasu a cikin kwana guda.

Rahoto ya nuna kusan mutum miliyan uku ne cutar ta kama a kasar, yayin da mutum dubu 77 da 583 suka rasu zuwa makon jiya.

Amurka za ta dawo wa Najeriya N80bn da ta ƙwato daga Diezani

Yadda gwamnati ta yi sulhu da ’yan bindigar Kaduna

‘Da kuɗin yankan farce na je Hajji’

Zambar Intanet: EFCC ta kama ’yan China 4 da wasu 101 a Abuja