Mai dafa wa Obama abinci ya mutu a kududdufi

Sai dai lokacin da ya mutu su Obaman ba sa gida

Mai dafa wa Obama abinci ya mutu a kududdufi

Obama

Mai dafa wa tsohon Shugaban Amurka, Barack Obama abinci, Tafari Campbell, ya fada wani kududdufi da ke kusa da gidan tsohon shugaban da ke Jihar Virginia, ya mutu.

Rundunar ’Yan Sanda ta Jihar Massachusetts, ce ta tabbatar da mutuwar Tafari, inda ta ce an ceto gawar mamacin ne daga wani kududdufi da ke Edgartown a Virginia ranaar Litinin.

Ya mutu yana da shekara 45. Ya mutu ya bar matarsa da ’ya’yansa maza tagwaye guda biyu.

Iyalan tsohon Shugaban ne dai suka dauke shi aikin dafa abincin. Sai dai sun yi tafiya ba sa gari lokacin da lamarin ya faru.

A cikin wata sanarwa ranar Talata, Obama da matarsa, Michelle, sun bayyana marigayin a matsayin “abin so gare su kuma amintacce.”

“Lokacin da muka fara haduwa da shi, kwararren mai dafa abinci ne a White House, mai basira kuma mai daukar abin da yake yi da muhimmanci,” in ji su Obama.

“A tsawon lokacin da muka shafe tare da shi, mutumin kirki ne, mai iya zama da mutane kuma ya zama bangarenmu.

“Dalili ke nan da lokacin da muke shirin barin White House, muka bukaci ya bi mu, kuma ya amince. Tun lokacin ya zama wani bangare na iyalinmu. Za mu dade muna jin takaicin rashinsa,” in ji tsohon Shugaban na Amurka.