Mai digirgire da duwatsu a kan keke a kasar Sin
Al’amari ne mai wuya mutum ya rika digirgire da manyan duwatsu a kansa lokacin da yake tukin keke, amma wani mai shekara 52, mai suna Zhang dunmu yana motsa jiki da duwatsu masu nauyin kilo 74, inda yake tukin keke.Zhang ya shafe shekara takwas yana wannan atisaye, inda yake share tsawon kilomita 10 yana tafiya […]
Al’amari ne mai wuya mutum ya rika digirgire da manyan duwatsu a kansa lokacin da yake tukin keke, amma wani mai shekara 52, mai suna Zhang dunmu yana motsa jiki da duwatsu masu nauyin kilo 74, inda yake tukin keke.
Zhang ya shafe shekara takwas yana wannan atisaye, inda yake share tsawon kilomita 10 yana tafiya da digirgire da duwatsu.
“A da ina son hawa keke ne da duwatsun a kaina, amma sai kawai na ji na damfaru da son wannan hanyar rayuwa,” inji shi.