Mai doki ya koma kuturi
Duniya rawar ‘yan mata ce domin na gaba kan koma baya. Wannan ne ya sa a zabubbukan da aka yi a kwanakin baya, jam’iyyar PDP da ke kan gaba a harkokin mulkin kasar nan, ta koma baya, domin kuwa al’amuranta sun balbalce, ta yi asarar jihohin da take tinkaho da su, har ma ta kai […]
Duniya rawar ‘yan mata ce domin na gaba kan koma baya. Wannan ne ya sa a zabubbukan da aka yi a kwanakin baya, jam’iyyar PDP da ke kan gaba a harkokin mulkin kasar nan, ta koma baya, domin kuwa al’amuranta sun balbalce, ta yi asarar jihohin da take tinkaho da su, har ma ta kai ta rasa gwamnatin tarayya, shugabanta kuma ya subuto. Dangane da haka ne ake cewa “Mai doki ya koma kuturi”, wasu kuma suke cewa “yaya babba ta sha kasa”.
Jam’iyyar PDP ta yi dagawa, ta kuma cika baki cewa ba za ta sha kasa ba a zaben da aka yi a ‘yan kwanakin baya, domin tana tinkaho da goyon bayan jama’a da kuma yawan gwamnatocinta na jihohi da ta tarayya. Ta dauka cewa tun da ta kiyasta cewa sai ta shekara sittin bisa mulki, tana damawa, talakawa na kurba haka nan, da dadi ko ba dadi, ba wani mai furzarwa, amma sai ga shi nan cikin shekaru shida kacal da ta yi tana gallaza wa bayin Allah, ta wargaje, talakawa kuma cikin sauki sun kwace goriba daga hannun kuturu mai fariya da izza.
An wayi gari wannan jam’iyyar da ta razana kowa a kasar nan, ta yi amfani da tsananin ikonta, na sama da na kasa, tana ta muzgunawa jama’a.Ta yi ta tsoma dogon hannunta a cikin randar dukiyar jama’a, har iyaka hammata, tana dumbuzo dukiyar talakawa, tana almubazzaranci da facaka da ita. Babu wani abin da ta tsinana cikin dogon lokacin da ta yi tana ta kankarar bayin Allah, ba ta kuma damu da wayyo-Allansu ba, balle ta tausaya masu, har ta dan tsagaita.
To a yanzu duk wadannan muggan kaba’iran da ta yi ta aikatawa sun kawo karshe cikin ikon Ubangiji.Domin kuwa cikin ruwan sanyi talakawa sun kwace goriba daga hannun kuturu.Bayan subutowar shugaban gwamnatin jam’iyyar da ta kafa, sa’anan kuma aka nuna mata iyakarta a wasu jihohin da aka kwakkwace daga hanunta don sakaci da lusarancin gwamnoninsu wadanda suka kasa tabuka wani abin-a-zo-a-gani duk kuwa da makudan kudaden da suka yi ta karba a madadin talakawansu don gudanar da ayyukan da za su inganta matsayin rayuwarsu.
Jam’iyyar PDP dai ta balbalce domin a zaben da aka yi a makon jiya na Gwamnonin jihohi ashirin da tara ta tashi da guda bakwai ne kacal, yayin da likkafar jam’iyyar adawa ta APC ta cilla sama, ta tashi da Gwamnoni kusan ashirin. Akwai alamun da suke nuna cewa idan har aka kammala bayar da sakamkon zaben wasu jihohi, ciki har da wanda aka soke dungurungum, jami’iyyar PDP za ta kara shiga wani mawuyacin halin da zai mayar da ita asfala-safilin.
Wannan yanayi da siyasar kasar ta shiga ya sa jama’a da yawa suna cewa dimokuradiyyar kasar nan ta balaga, domin kuwa a halin yanzu talakawa sun san ciwon kansu tunda dai a cikin ruwan sanyi suna iya yin amfani da kuri’unsu don kawar da gwamnatin da ba ta tabukawa wajen yi masu ayyukan alheri, su kuma cicciba wacce suke ganin za ta iya kai jirginsu gaci. A Arewacin Najeriya, inda talakawa suka fi tagayyara game da bakin mulkin jam’iyyar PDP, suka kuma gamu da matsalolin da suka janyo koma bayan tattalin arziki da rashin kwanciyar hankali da zaman lumana, jama’a na ta fatan cewa wannan canjin da aka samu zai zama mai amfani, ya kuma kawo karshen fitintinun da suka sha masu kai.
Lokacin da mutanen Arewaci suke wannan fata, sauran jama’an Najeriya ma suna yin addu’ar ganin cewa wannan mataki da aka dauka don samar da kwakkwarar jam’iyyar da ta maye gurbin ta PDP cikin dare guda, zai dore, ya kuma zama tafarkin da zai tabbatar da daidaituwar harkokin siyasa har a kai ga biyan bukatun al’ummomin da suka sadaukar da kai wajen kokarin kafuwar jam’iyyar APC.
Dangane da haka wajibi ne a bayar da cikakken goyon baya ga sababbin shugabannin gwamnatin tarayya da na jihohi, a kuma taya su da addu’ar taimakon Ubangiji, ba a tare a gindinsu ba, ana yi masu fadancin banza da na wofi, irin wanda akan yi wa mai kantu don a jefa shi a cikin ruwa. Wajibi ne fa su fahimci cewa fadawansu ne munafukansu, saboda haka nan sai su hanzarta guje wa makasansu domin suna nan manne da su. A yanzu za su rika ganin mutane iri-iri, da mai gaskiya da annamimi, da mai dadin baki da mai kulle-kulle a cikin zuciyarsa don ya cutar. Za su kuma ci karo da masu son kai, wadanda za su bayar da gurguwar shawara don amfanin kansu, da wadanda za su nemi a kifar, kowa ya rasa.
To, an dai ce soja shi ne malamin kansa, amma fa a fagen yaki. To yanzu wani sabon yakin ne aka kulla da azzalumai da masu kokarin hana ruwa gudu, ko masu son mayar da hannun agogo baya. Tilas ne sababbin shugabanni su tsara dabarun kaucewa daga masifu da matsalolin da jagororin jam’iyyar PDP suka ci karo da su, har santsi ya debe su, suka yi faduwar bakar tasa, tum, ba wani kara. A yanzu ne za su fara jin wasu shawarwari masu ban haushi ko ban takaici, wadanda ba da zuciya daya aka bayar da su ba, kuma idan aka gane, aka ki yin aiki da su, sai masu bayar da shawarar su koma gefe guda su yi ta yin jafa’i ko mugun alkaba’i, suna kokarin tsokano sama da kara don batanci.
Irinsu ne a cikin dan kankanen lokaci za su ja gefe, su fara guna-guni, suna cewa har yanzu ba a yi aikin komai ba, an bar jama’a suna shan wuya, kuru’un da suka bayar sun zama na banza. To, kada a kula da su, domin jan aikin da ke gaban sababbin mahukunta ja-wur ne; na yin gyara ga barnar da aka shisshirga ne a cikin lokaci dan kalilan, kuma sai an yi a tsanake, an dauki dogon lokaci kafin a gyara. Fatan da talakawa suka yi, shi ne sababbin shugabanni su kasance tamkar gwankin da ba ya dimuwa domin mai harbi.