Mai doki zai koma kuturi

An dade ana fama da matsi a kasar nan, kuma ma ko a halin yanzu da ake murna da samuwar gwamnatin canji matsi ya addabi kowa; ba kudi a birane da kauyuka, fatara ta kankama, ba wani mai jin dadi sai mahukunta da wadanda a ke  kira“duwatsun cikin ruwa ba su san ana rana ba.” […]

Mai doki zai koma kuturi
Mai doki zai koma kuturi

An dade ana fama da matsi a kasar nan, kuma ma ko a halin yanzu da ake murna da samuwar gwamnatin canji matsi ya addabi kowa; ba kudi a birane da kauyuka, fatara ta kankama, ba wani mai jin dadi sai mahukunta da wadanda a ke  kira“duwatsun cikin ruwa ba su san ana rana ba.” Talakawa na ta tagayyara, yunwa ta kusa fatattaka su. Rashin aikin yi ya zame ruwan dare, gidan kowa da alamunsa. Ta ko ina aka dubi lamarin sai a tabbatar da cewa, talakan Najeriya na yankayi cikin bakin talauci, yana kuma kururuwar neman agaji, duk kuwa da cewa, sabuwar gwamnatin da ya kafa da kuri’arsa na iyakacin kokarinta don saukakawa da taimaka masa wajen ficewa daga cikin kangin wahalhalun da gwamnatocin da suka shude suka wurga shi a ciki da rana tsaka.
Amma duk da haka nan sai ga ‘yan majalisun kasarnan na turzawa wajen neman karin albashi bisa wanda ake ganin yanzu ba mai karbar irinsa a cikin manyan jami’an kasar nan.
A halin yanzu dai idan ban da dattijan majalisar kasa da kuma ‘ya’yan majalisun wakilai da na dokoki da ke jihohi  da kansilolin kananan hukumomi babu wasu ma’aikatan da ke jin dadin rayuwa. Talakawa na sane da zancen da ake cewa ‘yan majalisun wakilai ke samun albashi da alawus tsagwagwan miliyoyin Nairori kowane wata, kuma duk da haka nan ba su gamsu ba, suna hankoron a yi musu kari, a kuma kyautata musu alawus-alawus dinsu, musamman ma na ababen hawa da na kama hayar muhalli..
To a yanzu ma dattijan majalisar kasa sun ce ba za a bar su a baya ba a batun neman karin kudin da ake biyan ‘yan majalisa tun da dai ba kanwa suka kawo kasuwa ba. Alawus din kowane katakoren dan majalisar dattijai ya kai Naira miliyan 45  bayan kowanne watanni uku  ko kuma a ce Naira miliyan 15 a kowane wata, a lokutan baya fa ke nan. To idan har suka yi nasarar samun karin da suke bukata kowannensu zai dinga tashi da Naira miliyan talatin ke nan a kowane wata, ko kuma idan aka yi gwari-gwari a ce Naira miliyan guda a kullu-yaumin.
Idan har aka kwatanta makudan kudin da ake biyan ‘yan majalisun Najeriya  da na wasu kasashe, sai a fahimci cewa, abin da ake biyan na Najeriya ya dara abin da talakawan wasu kasashen ke amsa nesa ba kusa ba, sa’annan kuma aikin da ‘yan majalisar Najeriya ke yi da tsawon lokacin da suka bata a  bakin aiki bai sa kwalliyar da ake yi biyan kudin sabulu ba.
Sa’ilin da ‘yan majalisun kasarnan za su kawo hujjar cewa ai daga cikin albashi da alawus din da ake biyansu akwai hakkin  wasu a ciki kamar wadanda sukan dauka aiki don taimaka musu wajen gudanar da ayyukansu, amma ai an rigaya an san cewa da yawa daga cikinsu ba su yin hayar ofisoshi a mazabunsu, ba su kuma daukar ma’aikatan da za su yi aiki a ciki. Wannan ne dalilin da ya sa ‘yan majalisar ba su biyan bukatun jama’ar da suka zabe su zuwa majalisu yin wakilci mai ma’ana.
Rashin sanin ya kamata ne zai kai dattijan majalisa da kuma wakilan jama’a a majalisun kasarnan su takarkare, suna neman a yi masu karin albashi da alawus-alawus din da a kan biya su loto-loto, a daidai lokacin da takwarorinsu na majalisun wasu kasashe ke daukar matakan rage albashinsu don su nuna damuwarsu ga tabarbarewar tattalin arzikinsu, da kuma gudummuwar da za su iya bayarwa don farfadowarsa.
A halin yanzu dai talaucin da ya yi katutu a kasarnan ya isa zama dalilin rage yawan dimbin albashin da ake biyan ‘yan majalisu, ba wai a daddage neman wani kari ba.‘Yan majalisun kasarnan na daga cikin rukunin wadanda aka fi biya albashi mafi tsoka a kasar nan. Ana iya cewa ma abin da ake biyansu ya dara wanda ake biyan manyan jami’an bankuna da kuma daraktocin kamfanonin mai.
Dangane da haka nan ana iya cewa wane irin gagarumin aiki ne ‘yan majalisun kasarnan ke yi da har za a dinga biyansu makudan kudi haka. To, idan kuwa har sun nace lallai sai an yi musu kari kan albashi da alawus  da suke dauka, kamar za su karya su, ba abin da zai hana ba za a ce da walakin ba, wai goro a miya, suna da  wata boyayyiyar manufa game da haka.
Ba shakka mun sha jin batutuwa game da yadda a kan ware wasu makudan kudi a cikin kasafin kudin shekara-shekara don yin wasu ayyukan da za su janyo wa ‘yan majalisun farin jini da sunan ayyukan a mazabunsu, amma sai daga karshe kudin su buge a aljiffan azzaluman ‘yan majalisan da za su yi sharholiya da su. Yawan kwanakin da ‘yan majalisu ke yi a bakin aiki,  bai kai wanda likitoci da malaman jami’o’i ke yi ba, amma idan aka kwatanta dan abin da ake biyansu da wanda ‘yan majalisa ke kwasa sai a tarar nasu cikin cokali ne, bai isarsu biyan bukatunsu na wata sai sun hada da wasu ‘yan dabarbaru. Abin da talaka ke da  sha’awar gani game da albashin ‘yan majalisun kasar nan shi ne a daddatse yawan albashin da ake biyansu ba wai a yi musu kari ba, domin babu wani dalilin da zai sa su nemi kari a wannan marrar ta haihuwar guzuma: da kwance, uwa kwance.
Ba ma sai an je da nisa ba don neman dalilan da ya sa ‘yan majalisunmu suka daddage neman karin albashi da alawus ba a wannan mawuyacin hali, ganin cewa darajar man fetur din da gwamnati ta dogara a kai don samun kudin biyan bukatunta, suna so ne tun da wuri su gina kansu don zaben 2019, idan kuma ba su biyan bukata ba su goga wa Gwamnatin Muhammadu Buhari da shi kansa kashin kajin da zai sa jama’a su guje shi, suna tottoshe hancinsu saboda doyi. To amma ai wannan ba dalili ne ba da zai sa su nemi karin albashi, domin kuwa abin da talakawan Najeriya suka fi damuwa da shi a halin yanzu, shi ne, dabarun da wakilansu za su iya bi don kawo canjin da zai magance matsalolin da suka hadasa karayar arzikin da ya jefa su cikin kunci da matsi.
Wannan bukatar karin albashi da alawus da ‘yan majalisunmu suka kawo a yanzu ta yi kama da hankoron tsiyata kasar a fafutikarsu mara kan-gado ta neman gina kansu tun da sanyin safiya saboda su samu sukunin sake tsayawa zabe ko ana ha-maza-ha-mata.
Lallai kuwa ‘yan majalisunmu sun isa marasa kishin kasa, domin sun nuna mana a zahiri sun fi son kansu fiye da kasarsu da kuma talakawan cikinta da suka ba su damar zuwa majalisa don su azurta kawunansu. Kamata ya yi talakawa su ja kunnuwan wakilansu muddin dai ba fin karfinsu suka yi ba, domin daga karshe talaka ne gari zai waya, wanda ya zaba don ya wakilce shi zai yi ta kudancewa, shi kuwa yana ta talaucewa. Idan ba haka ba kuwa to mai doki zai koma kuturi.