Mai doya
Wata rana ce wani alkali yana warware wata shari’a, kansa ya yi zafi sai wani bakauyen mai tallar doya ya zo wucewa, ya leko cikin kotun ya ce: “A sai doya!” Alkali ya ce a zo masa da mai doya. Ya ce masa: “Ka san ko surutu ba a yi a kotu amma ka zo […]
Wata rana ce wani alkali yana warware wata shari’a, kansa ya yi zafi sai wani bakauyen mai tallar doya ya zo wucewa, ya leko cikin kotun ya ce: “A sai doya!” Alkali ya ce a zo masa da mai doya. Ya ce masa: “Ka san ko surutu ba a yi a kotu amma ka zo kana tallar doya? Saboda haka za a daure ka a gidan yari tsawon wata uku.” Mai doya ya ce: “Daga cewa a sai doya?” Sai alkali ya ce: “Wata shida.” Mai doya ya sake cewa: “Doya fa na ce a saya.” Sai alkali ya ce: “Wata tara.” Ran mai doya ya baci, sai ya ce: “To a sai doyoyi.”
Daga Usman dangundumar Jama’are, 08163055770