Mai fama da ciwon kai da ya rayu da harsashi a kansa shekara 20

Matashin, ya dade yana fama da ciwon kai wanda ba zai iya tuna lokacin da ya tsaya ba.

Mai fama da ciwon kai da ya rayu da harsashi a kansa shekara 20

Hoton kokon kan mutum da harsashi a cikinsa Hoto: Times of India

Wani matashi dan kasar China da yake fama da matsanancin ciwon kai a bayabayan nan, ya kadu matuka da ya samu labarin cewa, ya shafe shekara 20 yana rayuwa da harsashi a gefen hagu na kokon kansa.

Matashin mai suna Diao Chen mai shekara 28 daga yankin Shenzen, ya dade yana fama da ciwon kai wanda ba zai iya tuna lokacin da ya tsaya ba, sai dai a baya-bayan nan ciwon ya kara tsananta.

Da farko, Chen ya yi tunanin cewa, ciwon ya samo asali ne saboda rashin isasshen barci a ranakun mako, amma daga bisani ya gano barci ba shi ne matsala ba, musamman yadda ciwon kan kan tashi da daddare.

A karshe, ciwon ya yi tsamari sosai har ya yanke shawarar zuwa asibiti, inda likitoci suka gano wani abu mai ban-mamaki da ke kawo ciwon.

Yayin da likitocin suka yi amfani da na’urar daukar hoton jikin mutum ta MRI a babban asibitin Jami’ar Shenzhen binciken binciken ya gano wani bakon abu da ya makale a gefen hagu na kan Diao Chen.

Da aka duba a hankali sai aka gano wani karamin harsashi na karfe, don haka ma’aikatan asibitin suka tambayi majinyacin ko yana da masaniyar yadda abin ya same shi.

Wani abin sha’awa, Chen ya tuna cewa lokacin da yake dan shekara 8, shi da dan uwansa suna wasa da wata karamar bindiga a gida, sai bindigar ta tashi bisa kuskure, ta harbe shi a gefen kai.

Shi da dan uwansa suna tsoron kada iyayensu su hukunta su, don haka ba su ce komai ba. Kuma gashin kai ya rufe raunin, don haka iyayen ba su iya gano abin ba.

Duk da haka, raunin bai yi muni sosai ba, don haka a karshe ya manta da shi. Likitoci sun bayyana wa matashin mai shekara 28 cewa, ya yi sa’a da ya rayu, saboda harsashin yana kusa da goshi da kunne, amma bai shiga cikin kokon kan ba, kuma bai taba kwakwalwa ba.

An yi masa tiyatar gaggawa a karshen watan jiya kuma an yi nasarar cire harsashin mai shekara 20 a jikinsa, wanda tsawonsa ya kai sentimita daya.

An sallami Chen kuma yana samun sauki a gida. Wannan labari mai ban mamaki ya tuno da wani lamari makamancin haka da muka gabatar a baya-bayan nan, game da wani mutum da ya rayu da cokali a cikin hanjinsa tsawon shekara guda, ba tare da saninsa ba.