Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano

Gwamnatin Kano ta jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa tana mai jaddada aniyar gudanar da bincike.

Mai gari ya tsere bayan mazauna sun cinna wa gidansa wuta a Kano

A yayin da rikici ya kaure cikin dare tsakanin jami’an tsaro da masu gine-gine a unguwar Rimin Zakara, mutane sun cinna wa gidan mai garin wuta.

Da farko dai an samu rikici tsakanin mahukunta da mutanen yankin, lamarin da ya kai ga mutuwar mutane huɗu tare da ƙone gidan mai unguwar.

Aƙalla wasu mutum huɗu sun riga mu gidan gaskiya sakamakon ƙazamin rikicin da ya hautsine tsakanin mahukunta da mazauna unguwar Rimin Auzinawa da Rimin Zakara da ke Ƙaramar Hukumar Ungogo a Jihar Kano.

Bayanai sun ce an harbe mutanen huɗu ne yayin da suka fito tirjiya kan rusau ɗin gine-ginensu da jami’an hukumar tsara birane ta Jihar Kano KNUPDA suka aiwatar.

Majiyoyi sun shaida wa Aminiya cewa galibin gidajen da rusau ɗin ya shafa tuni KNUPDA ta shafa musu alamar cewa aiki zai biyo ta kansu.

Ana dai zargin cewa gine-ginen aƙalla 40 da mahukuntan suka rushe an yi su ne a kan fulotan Jami’ar Bayero da ke Kano.

Sai dai wani mazaunin yankin da ya zanta da Aminiya, ya ce tun da jimawa Hukumar ta KNUPDA ta warware wannan matsala kuma ta jaddada musu cewa a halastaccen matsuguninsu suke domin bai shiga harabar jami’ar ba.

“Mun jima da warware wannan matsala da KNUPDA. Sun tabbatar mana cewa gine-ginenmu ba su shiga harabar jami’ar ta Bayero ba.

“Amma kwatsam sai ranar Lahadi da daddare jami’an KNUPDA suka zo suka fara rusau.

“A yayin da wasu daga cikin mazauna suka yi ƙoƙarin tirjiya ne suka harbi mutum huɗu da yanzu an yi musu jana’iza. Wannan abun takaici ne.

Aminiya ta yi ƙoƙarin jin ta bakin Manajan Darekta na KNUPDA amma lamarin ya ci tura.

Kazalika, wakilinmu da ya ziyarci ofishin KNUPDA ya tarar da shi fayau a yayin da duk manyan jami’an sun ƙauracewa zuwa aiki sakamakon fargabar abin da ka iya zuwa ya komo kamar yadda wani ƙaramin ma’aikaci ya tabbatar.

“Ana cikin wani yanayi na fargaba a ofishin nan. Shi ya sa ko wurin ajiyar motoci ya zama fayau don duk manyan ma’aikatan babu wanda ya shigo.

“Yanzu haka ƙananan ma’aikata ne kawai suke zaman dabaro a ofishin ba tare da sanin madafar da za a kama ba.

Wani babban Darektan KNUPDA da Aminiya ta tuntuɓa, ya ce ba ma’aikatansu ne suka yi rusau a unguwar ba, inda ya ba da tabbacin cewa jami’ai ne daga Ma’aikatar Ƙasa da Tsara Birane ne suka aiwatar da aikin.

Haka kuma, wani jami’i daga ma’aikatar wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya ce wuraren da aka yi rusau mallakin Jami’ar Bayero ne kuma nan gaba kaɗan za a fitar da sanarwa a hukumance.

Mutum uku ne suka mutu — Gwamnatin Kano

Gwamnatin Kano ta bakin Kwamishinan Labarai, Ibrahim Abdullahi Waiya, ta tabbatar da cewa mutum uku ne suka mutu yayin da jami’an tsaro aƙalla 30 suka jikkata a sanadiyyar tankiyar da auku a dalilin rusau ɗin.

Kwamishinan ya bayyana cewa tun farko Jami’ar Bayero ce ta nemi gwamnatin ta shiga lamarin, wanda jami’an tsaro da suka haɗa da ’yan sanda, DSS da na Sibil Difens suka yi ruwa da tsaki.

Waiya ya ce an shafe fiye da shekaru 40 ana wannan kwakwazo kan halascin mallakar fulotan tsakanin mazauna yankin da kuma jami’ar ta Bayero.

Sai dai ya ce jami’ar ta fuskanci ƙalubale a ƙoƙarin da ta riƙa yi don ganin ta karɓe haƙƙinta duk da gargaɗi da wa’adin da aka bayar na neman mazaunan su tashi.

Kwamishinan ya bayyana rashin jin daɗinsa dangane da salwantar rayukan da aka samu duk da cewa mazauna yankin sun wuce gona da iri.

Sai dai a cewar Kwamishinan, kundin tsarin mulkin Nijeriya ya bai wa jami’an tsaro ’yancin kare kansu a duk lokacin da rayuwarsu ta fuskanci barazana.

Ya kuma jajanta wa iyalan waɗanda lamarin ya shafa da cewa gwamnati za ta gudanar da cikakken bincike a kan lamarin.