Mai garkuwa da mutane ya nemi ya kashe kansa bayan an ritsa shi

Ya ce, “Na so na kashe kaina ne saboda kada jami’an tsaro su yi min tambayoyi.

Mai garkuwa da mutane ya nemi ya kashe kansa bayan an ritsa shi

Wani shugaban masu garkuwa da mutane, Mohammed Gidado, da ake nema ruwa a jallo a Jihar Taraba ya yi yunkurin kashe kansa, yayin da jami’an tsaro suka yi arba da shi.

Ko da ya tabbatar jami’an tsaron hukumar NSCDC sun yi masa kofar rago, sai ya zaro wata sharbebiyar wuya ya fara yanka makogaronsa, amma suka yi wuf suka kwace ta kafin ya gama yaka wuyan nasa.

Kwamandan NSCDC na Jihar Taraba, Muhammed Waksha, ya tabbatar da cewa an kama babban mai garkuwa da mutanen tare da wasu yaransa ne a yankin Jebjeb da ke Karamar Hukumar Karim Lamido, a Jihar.

Ya ce an jami’an hukumar sun yi musu kofar rago ne a yayin da suka tare titin da ya yi iyaka da jihohin Filato, Bauchi da kuma Gombe.

Sun kuma jima suna ta’asa tare sa addabar Jihar Taraba da fashi da makami, satar mutane, satar dabbobi da sauransu.

Kwamandan, ya kara da cewa bincikensu ya gano cewar akwai sauran wasu yaran Mohammed Gidado da suka rage kuma jami’ansu na ci gaba da bincike don gano maboyarsu.

Mohammed Gidado, wanda ake zargin ya dade yana harkar satar mutane ya ce, “Mun jima muna tare mutane tare da kwace musu dukiyoyinsu a tsakanin iyakar Jihar Filato da Taraba.

“Muna da yawa, amma na samu labarin an kashe mutanenmu da yawa a arangamarsu da jami’an tsaro.

“Na so na kashe kaina saboda kar jami’an tsaro su yi min tambayoyi. Mutane na karshe da muka yi garkuwa da su mun karbi N500,000 a wajensu”, inji shi.

Har wa yau, an cafke wasu mutum hudu da suka kware wajen satar shanu da yin garkuwa da mutane a wasu sassa na Jihar ta Taraba.

Lakurawa sun kashe ma’aikatan kamfanin Airtel 3 a Kebbi

Matashi ya kashe mahaifiyarsa don yin tsafi a Kuros Riba

DSS ta ceto mutum 4 da aka sace a Sakkwato

2025: Wutar lantarkin Najeriya ta ɗauke gaba ɗaya