Mai gida ya sallami ‘kiya-teka’ kan ƙara kuɗin haya

Wani mai gida ya zaftare rabin kuɗin haya tare da sallamar kiya-tekan gidansa saboda ƙara kuɗin haya ba da izininsa ba

Mai gida ya sallami ‘kiya-teka’ kan ƙara kuɗin haya

Wasu daga cikin gidaje da gwamnati ta gina a baya

Wani mai gidan haya ya rage kuɗin haya tare da korar ‘kiya-tekan’ gidansa  saboda ƙara kuɗin haya ba da izininsa ba.

Mai gidan ya kori kiya-tekan ne bayan da ya gano cewa ya ƙara wa ’yan haya kuɗi a ɓoye kuma yana cinye kuɗin, a garin Asana, fadar Jihar Delta.

Daga nan ya zaftare wa ’yan hayan rabin kuɗin hayan da suke biya, wanda ’yan hayan suke kukan cewa ya yi tsada.

A baya wasunsu na biyan N600,000 a kan gida mai ɗakuna biyu da falo, masu ɗaki uku da falo kuma suna biyan N1,000,000.

Amma yanzu mai gidan ya mayar da kuɗin hayan kowannensu N350,000, ba tare da la’akari da wani bambanci ba.

Mai gidan ya bayyana cewa ya zaftare kuɗin hayan ne bisa la’akari da tsadar rayuwa da ake fama da ita a Nijeriya a halin yanzu.