Mai Gidan Gilashi ba ya jefe-jefe

Sa’ilin da aski ya zo gaban goshi game da damabarwar kawo karshen ta’addancin kungiyar Boko Haram, sai kuma ga wata sabuwar fitina can ta kunno kai a yankin Kudu-maso-Gabashin kasar nan. Ba za a iya cewa wannan fitinar sabuwa fil ce ba, domin kuwa an dade da ita, kusan shekaru fiye da 50, amma a […]

Mai Gidan Gilashi ba ya jefe-jefe
Mai Gidan Gilashi ba ya jefe-jefe

Sa’ilin da aski ya zo gaban goshi game da damabarwar kawo karshen ta’addancin kungiyar Boko Haram, sai kuma ga wata sabuwar fitina can ta kunno kai a yankin Kudu-maso-Gabashin kasar nan. Ba za a iya cewa wannan fitinar sabuwa fil ce ba, domin kuwa an dade da ita, kusan shekaru fiye da 50, amma a wannan marrar ce ta yi kamari, take kuma neman ta sake tayar da hankulan jama’a kamar yadda ta taba yi shekaru aru-aru, har hakan ya kai ga yakin basasa.

Watanni kadan bayan kisan gillar da aka yi wa shugabannin Najeriya, musamman ma ‘yan Arewa da kuma na kasar Yarbawa, hakan kuma ya kai ga kafa gwamnatin mulkin soja a karkashin Janar Johnson Thomas Amunikwe Agwuyi Ironsi, dan kabilar hafsoshin da suka hambarar da gwamnatin farar hula, ‘yan Arewa sun nemi lallai sai an yi wa wadancan azzaluman hafsoshin haddi, amma sabon shugaban kasa, Agwuyi Ironsi ya kekasa ya ki, ya kuma kare su a gidan jarun don kada masu neman daukar fansa su kai gare su. Daga bisani ne kuma Janar Ironsi ya dinga fito da maitarsa a fili, har sai da ta kai ya kafa wata dokar soja mai lamba ta 32 da nufin dunkule kasar karkashin gwamnati guda. Don hakan ya bayar da dama ga ‘yan kabilarsa su ji dadin hawan kawara ga sauran kabilun kasar nan, suna sukwanar su yadda suka ga dama.
Wannan al’amarin ya kara tunzura ‘yan Arewar da suka fito, suka yi zanga-zangar nuna kin amincewa, suna cewa da su kasance a karkashin wannan yanayin ai gara a raba kasar, wasu kuma na cewa ai ya wajaba Arewa ta ware, domin bisa ga dukkan alamu ba a kaunarsu a fadin Tarayyar Najeriya, ganin irin muzgunawa da kyamar da ake nuna musu a harkokin mulki da na zamantakewa.
To, amma ba a Arewar ce ba kadai aka sha tabo batun warewa daga kwaryar Tarayyar Najeriya ba. A 1954 ma Cif Obafemi Awolowo ya taba tabo wannan batun sa’ilin da aka kI amincewa da shawarwari guda shida da ya kawo a wajen taron tsara sabon kundin mulkin Najeriya da zai bayar da dama a kakkafa majalisun dokoki na jihohi, yayin da ya ce idan ma haka ne to ya kamata a cikin kundin tsarin mulki a kafa wata dokar da za ta ba kowace jiha ‘yancin ficewa daga Tarayyar Najeriya a dukkan lokaci da ta ga haka shi ne mafi a’ala a gare ta.
Shugabannin Arewa na wancan lokacin sun yi aiki da hankali, wanda ya fi aiki da agogo, wajen nuna wa jama’ar Arewa muhimmancin ci gaba da zama a kasa daya, dunkulalliya, wacce za ta kunshi dukkan kabilun cikinta wuri guda don kowacce ta bayar da gagarumar gudummawa wajen gina kasa.
Mutanen Arewa sun kau da kai, sun hakura, sun gwammace a ci gaba da zaman tare, amma saboda taurin kan wasu shugabanni, ‘yan kabilar Kudu-maso-Gabas, hakan bai yiwu ba, sai da ta kai su ga ware yankinsu da yanzu ya hada da shiyyoyin Kudu-maso-Kudu da kuma Kudu-maso-Gabas, suka kuma fice daga kwaryar Jamhuriyar Tarayyar Najeriya, abin sai da ya kai ga yakin basasan da aka fafata da su na tsawon watanni 30, wanda ya yi sanadiyyar asarar rayuka kusan miliyan uku a dukkan bangarorin, kafin su hakura, su zauna tare da sauran jama’ar kasar nan. Amma duk da irin karimcin da aka yi masu bayan kammala basasan, da kuma irin adalcin da aka gwada musu, da taimakon da aka ba su don su tashi, su nemi na kansu, su zamanto daidai da kowa, ba su amince da yadda sauran al’ummomin kasar nan suka rungume su hannu bibbiyu ba, ba su kuma nuna godiyarsu da irin karimcin da aka yi musu ba, sai suka ci gaba da nuna hali irin na barden goyo, wanda ke gatsa wa mai goye da shi cizo.
Haka nan aka yi ta tafiya, duk gwamnatin da ta zo, walau ta soja ce ko ta farar hula sai ta nemi dadada musu, ta kuma nuna wa duniya cewa durkusa wa wada ba gajiyawa ba ne. Amma su ba su san haka ba, a ko da yaushe kokarinsu, shi ne, yadda za a daga musu kafa su ji dadin mike tasu kafar don mulkar Najeriya yadda suke so, ta yadda zai zamanto su ne za su mamaye dukkan harkoki, kuma sai yadda suka ga dama za su dama, su ba kowa ya kurba haka nan. Wadannan mutanen sun yi karfi a zamanin tsohon Shugaba Goodluck Jonathan, wanda suka mayar da gwamnatinsa tamkar tasu, sai abin da suke so za ta aikata, kuma su ne suka yi kaka-gida cikin manyan jami’an da ke karkata akalarta. Sun kokarta ainun don Gwamnatin Jonathan ta dore, ta yadda za su ji dadin ci gaba da tatse arzikin kasar da suka yi wa karkaf, suka bar ta ba ko karfanfana.
A wancan zamani sun bidi canja tsarin Najeriya yadda za ta dace da manufa da alkiblarsu idan sun danki ragamar mulki bayan saukar Jonathan, amma suna tasu ce Allah kuma na Nasa. Da suka ga mulki ya kubuce a hanunsu, sakamakon rashin adalcinsu da kuma zaluncinsu, sai suka dukufa wajen muzguna wa sabuwar Gwamnatin Muhammadu Buhari, suna cewa, ta mayar da su shanun ware a dukkan mukaman da ta rarraba, daga bisani bayan sun fahimci inda gwamnatinsa ta dosa sai suka fara daga hakarkari, kungiyoyin farfado da Biafra MOSSOB da kuma ta IPOB suka yi ta shirya zanga-zangar da za ta iya janyo fitinar da za ta dakile manufofin sabuwar gwamnati, ko kuma su taka wa jagoranta birkin da zai kawo cikas a ayyukan alherin da yake yi wa al’umma.
Ya kamata shugabannin wadanan kungiyoyin su fito fili, su ja musu kunnuwa, su nuna musu cewa ba su kadai ne ba ke da korafi game da halin da kasar nan ke ciki. Sa’anan kuma ba su ne kadai ke da ‘yancin fitowa su yi zanga-zangar kin amincewa da kasancewa cikin kasar nan ba, kowane bangaren kasar nan na iya yi, amma bisa lumana da kwanciyar hankali. Idan har kowa da kowa zai fito ya ce lallai sai a raba kasar, su wane ne za su fi kwaruwa? Ai wadanda ke tunkaho ne cewa arzikin da ke warwatse a dukkan sassan kasar nan na hannunsu. To idan kuwa haka ne sai su yi la’akari da cewa mai gidan da aka yi da gilashi bai yin jifa da dutse, don kar jifarsa ta fasa masa gilashin, ko idan an mayar da martani gilasan su ratsattsake.