Mai Goje ya zama sabon Sakataren SEMA na jihar Yobe
Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni, ya tabbatar wa da Dokta Muhammad Mai Goje mukamin sabon zababben Sakataren hukumar bada agajin gaggawa SEMA ta jihar. Kafin nadin na Dokta Mai Goje, a wannan mukami Jami’i ne mai aikin jinkai kuma kwarare a bangaren allurar rigakafi, a cibiyar lafiya ta CHAI Clinton Health Access Initiative, […]
Gwamnan jihar Yobe Alhaji Mai Mala Buni, ya tabbatar wa da Dokta Muhammad Mai Goje mukamin sabon zababben Sakataren hukumar bada agajin gaggawa SEMA ta jihar.
Kafin nadin na Dokta Mai Goje, a wannan mukami Jami’i ne mai aikin jinkai kuma kwarare a bangaren allurar rigakafi, a cibiyar lafiya ta CHAI Clinton Health Access Initiative, da suke samun tallafin gidauniyar Bill da Melinda gate a jihar Yobe.
Wannan mukamin na zababben Sakataren hukumar ta SEMA da aka ba shi zai fara aiki ne nan ta ke.