Mai gyaran farce ta shafe shekara 30 ba ta yanke nata ba
Rabonta da yanke farce tun 1989
Wata kwararriya a fannin gyaran farce mai suna Cordelia “Dee Dee” Adams, ’yar asalin birnin Gary da ke Jihar Indiana ta kasar Amurka ba ta yanke farcenta ba a sama da shekara 30, inda yanzu aka auna tsawonsa ya fi inci 12.
Cordelia Adams mai shekara 59, ta ce farce wani abu ne da ya kamata a gani.
- Daraktan shirin Izzar So ya rasu
- Jamus za ta dawo wa Najeriya kayan tarihin da ta sace shekara 120 da suka wuce
Ba wai kawai an rufe su da nau’o’in jan farce ba masu nuna zane-zane iri-iri ba, amma duk sun wuce tsawon inci 12.
Ta fara barin faratan ne a 1989, lokacin da ta zama kwararriyar mai kwalliyar farata.
Kuma ta koya wa kanta yin kowane irin aiki na yau da kullum da hannuwan ba tare da ta raunata faratan ba.
Kamar yadda kuke tsammani, Adams tana samun kulawa sosai saboda faratan nata, amma wannan shi ne ainihin bangaren da ta fi so game da samun farata masu tsawo da ba a saba gani ba.
Abin da ya fi dacewa game da samun dogayen farata shi ne mai da hankali da Cordelia ta yi game da su kamar yadda ta bayyana wa kafar labarai ta Truly.
Ta ce mafi munin abin da ta ji game da faratan shi ne tambayoyin rashin mutunci da mutane ke yi mata a wasu lokuta, kan yadda take cin abinci ko take kula da kanta da wadannan farata.
Ta yi ikirarin cewa, a cikin shekara 30 na girman faratan hannunta, ta koya wa kanta yin duk ayyukan yau da kullun ba tare da lalata faratan ba.
Ta koyi yadda za ta yi rubutu cikin kiyayewa da kuma tukin mota da rike abubuwa a hannun, ba tare da faratan sun karye ba.
“Tsawon faratan ya ninka tsawon hannuna, don haka idan na rike wani abu suna yin wani bangare gaba daya. Ba na zuwa wajen karin farata,” inji Adams.
Kodayake tana iya yin mafi yawan abubuwa na yau da kullum kamar na wanda bai da tsawon farata, dole ta daidaita wasu ayyukanta na yau da kullum, kamar amfani da wayar salula ko yin wanki.
Duk da haka, ba ta ganin kanta a matsayin mai dogayen farata kawai saboda za su sa rayuwarta ta fi dacewa da bukatarta.
Abin mamaki shi ne, kwararriyar mai gyaran farcen ta samu damar kiyaye fasahar farcen hannunta a cikin kyakkyawan yanayi wanda idan wadansu ne suna iya kodewa ko su iya karyewa, yayin da wasu ayyukanta suke iya daukar shekara biyar.