Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Duk wanda ya yi arba da wani matashi xan kimanin shekara 40 da ke sana’ar yin faskaren itace a garin Kafanchan sai ya tsaya ya sake kallon sa cike da mamaki

Mai hannu ɗaya da ke sana’ar faskare

Duk wanda ya yi arba da wani matashi dan kimanin shekara 40 da ke sana’ar yin faskaren itace a garin Kafanchan sai ya tsaya ya sake kallonsa cike da mamaki, ganin yadda ake samun wasu matasa da yawa dake da cikakken ƙarfi da lafiya amma suke zaman rashin sana’a a cikin al’umma.

’’Mutane da dama suna mamaki a duk lokacin da suka fara ganina a karon farko ina faskaren itace da hannu ɗaya.

“A sanadiyyar haka ma na sha samun kyaututtuka daban-daban daga mutane iri-iri da suke cewa ina burge su,” inji Sunday Bulus.

“Akwai wanda ya ba ni kyautar babbar waya saboda na burge shi a lokaci guda kuma na ba shi tausayi.

“A haka nake samun mutane iri daban-daban dake tausaya min ganin irin halin da nake ciki na lalura amma hakan bai kashe min zuciya ba.”

Mista Sunday Bulus, dan asalin Unguwar Bayan Loko da ke yankin Kafanchan kewaye ya ce bai daɗe da fara sana’ar ta faskare ba, domin yanzu shekararsa ɗaya da farawa “kamar wasa wani ya tsokane ni ko zan iya yi masa faskare a gidansa in zo in yi zai biya ni.

“Na ce masa ƙwarai kuwa mai zai hana, ban taɓa yi ba amma na amsa masa kuma na je na yi masa tsaf, nan take ya biya ni ya kuma buƙaci na ci gaba da zuwa ina yi yana biya na.

Daga nan aikin ya kankama inda wasu suka fara gayyatarsa musamman masu sayen itatuwa don su faskara su siyar.

Ya ce ya kan yi faskaren Naira dubu uku a rana idan akwai aiki don ba kullum ake samun aikin ba.

Ya ce iyakar karatunsa ya tsaya ne a karamar sakandare inda ya kammala aji uku amma bai samu damar ci gaba da karatu ba saboda rashin mai ɗaukar nauyinsa.