Mai hannu daya ya zama zakara a wasan daga karfe mai nauyi
Wani nakasasshe dan kimanin shekara 20 da ke zaune Amurka mai suna Luke Ericson ya zama zakara a gasar daga karfe mai nauyi da wata cibiya mai suna Cross Fit Tournament ta shirya. Gasar wadda ta hada nakasassu da wadanda ba nakasassu ba a wasanni daban-daban da suka hada da daga karfe mai nauyi (wightlifting) […]
Wani nakasasshe dan kimanin shekara 20 da ke zaune Amurka mai suna Luke Ericson ya zama zakara a gasar daga karfe mai nauyi da wata cibiya mai suna Cross Fit Tournament ta shirya. Gasar wadda ta hada nakasassu da wadanda ba nakasassu ba a wasanni daban-daban da suka hada da daga karfe mai nauyi (wightlifting) da hawa igiya da lankwashe-lankwashe da sauransu, Mista Ericson ne ya zama zakara a bangaren daga karfe mai nauyi.
Nakasasshen yakan yi abin da ba kasafai masu hannu biyu za su iya yi ba. Hasalima a duk lokacin da yake wasa dubban ’yan kallo ne ke tururuwa don su kashe kwarkwatar ido don ganin yadda Ericson yake nuna bajinta.
Rahotanni sun nuna an haife shi ne da hannu daya, don haka tun yana karami bai taba yin amfani da hannaye biyu ba balle ma a ce daga baya ne nakasar ta same shi.
Jama’a da dama sun barke da murna a lokacin da aka bayyana Ericson a matsayin wanda ya zama zakara a gasar daga karfe mai nauyi. Nan da nan kafofin watsa labarai suka rika cincirindon tattaunawa da shi saboda namijin kokarin da ya nuna duk da nakasar da ke damunsa.
Da aka tambaye shi yadda yake ji idan ya daga karfe mai nauyi da hannu daya sai ya ce “bambancin kawai shi ne yadda zan daidaita karfen a kafadata kafin na daga, don akwai wahala wajen daidaita abin da na dauka a kafada da hannu daya maimakon masu hannu biyu, amma in ban da haka ban fuskantar wata matsala”.
Mista Ericson ya ce bai taba daukar nakasar da ke damunsa a matsayin lalura ba, sai dai wata hanya ce da take karfafa masa gwiwar yin duk abin da ya sanya a gaba.
A lokacin da yake hira da wata mujalla mai suna Inside Edition a Amurka, ya ce “kasancewata nakasasshe mai hannu daya tamkar wata baiwa ce daga Allah, don hakan na karfafa mini gwiwar yin wadansu ayyukan da ke sa masu hannu bibbiyu su rika yin koyi da ni, don na zama tamkar abin koyi a duk wasannin da nake gudanarwa.
Baya ga wasan daga karfe mai nauyi Ericson yakan shiga wasan hawa igiya, da na tsalle-tsalle da kuma na lankwashe-lanwkashe.