Mai haura gidajen mutane na yi wa mata fyade ya zo hannu

Wani saurayi da ake zargi da haura gidajen matan aure da niyyar yi musu fyade ko kwace dubunsa ta cika. Saurayin mai suna Abdullahi Isma’ila da aka fi sani da Gajeren Wando mai kimanin shekara 25 yana zaune a gida mai lamba 31 a Layin Imamu da ke Tudun Wada, Zariya.Aminiya ta gano cewa ana […]

Mai haura gidajen mutane na yi wa mata fyade ya zo hannu

Abdullahi mai gajeren wando tare da wukarsaWani saurayi da ake zargi da haura gidajen matan aure da niyyar yi musu fyade ko kwace dubunsa ta cika. Saurayin mai suna Abdullahi Isma’ila da aka fi sani da Gajeren Wando mai kimanin shekara 25 yana zaune a gida mai lamba 31 a Layin Imamu da ke Tudun Wada, Zariya.
Aminiya ta gano cewa ana zargin matashin ya shahara wajen aikata miyagun laifuffuka inda sau da yawa an sha kama shi ana tura shi gidan maza amma bai daina ba.
Shubagan ’Yan sintiri na yankin Zariya, Alhaji Kabiru Ahmad da ya jagoranci kama saurayin ya shaida wa Aminiya cewa da misalin karfe biyu na dare suna aikin tsaron gari, sai wani abokin da ke Layin Sardauna a Tudun Wada Zariya ya kira shi ta waya ya ce su kai musu dauki ’yan fashi sun shiga gidansu. “Koda isowarmu sai muka kewaye gidan, to, dama mazauna gidan sun kama wannan yaro mai gajeren wando da zuwa muka karbe shi, muka tambaye shi ko tare da wasu yake. Ya ce mana shi kadai ne da ma mun samu labarin ba ya tafiya da kowa, sai muka kai shi ofishin ’yan sanda domin su ci gaba da bincike a kansa. Ya ce a can ne mutane suka fara bayyana domin gabatar da irin abin da yaron ya aikata a gidajensu.
daya daga cikin wadanda Abdullahi Mai gajeran wando ya shiga gidansu ya yi artabu da iyalinsa mai suna Dokta Ahmed Bello da ke Tsangayar Koyar da Lissafi a Jami’ar Ahmadu Bello da ke Kongo, Zariya ya ce kamar yadda matarsa ta shaida masa bayan an kama shi a gidan makwabtanmu ta tabbatar da cewa shi ne ya shiga ya tsare ta tare da ’ya’yanta da doguwar wuka ya kwace wayoyinsu da gwala-gwalai da kudi da na’urar kwamfuta ya gudu, kuma ya yi barazanar cewa idan ba su yi hankali ba zai halaka mai gidansu domin dama turo shi aka yi.
Wani jami’in tsaro da ya nemi a sakaya sunansa ya shaida wa Aminiya cewa sun taba kama matashi wata biyu da suka wuce dalilin shiga gidajen malaman makaranta da dakunnan dalibai yana firgita su, bayan sun kammala bincikensu suka mika shi ga ’yan sanda iya abin da zan iya tunawa ke nan.
A lokacin da Aminiya ta ziyarci ofishin ’yan sanda na Tudun Wada, Zariya sun tabbatar mata da kama matashin sai dai sun ce har yanzu suna tattara bayanai a kansa kafin su dauki matakin da ya dace.