Mai hoto ya maka Tuface kotu don a biya shi Naira miliyan 120

Wani mai sana’ar hoto, wanda ya ce sunan Emmanuel Okolo ya maka shahararren mawakin zamanin nan, Tuface Idibia da matarsa, Annie Macaulay kotu, inda ya bukaci a biya shi diyyar Naira miliyan N120 saboda aikin daukar hotunan da ya yi a yayin bikin auren mawakin. Mai hoton dai ya yi ikirarin cewa an dauke shi […]

Mai hoto ya maka Tuface kotu don a biya shi Naira miliyan 120
Mai hoto ya maka Tuface kotu don a biya shi Naira miliyan 120

Wani mai sana’ar hoto, wanda ya ce sunan Emmanuel Okolo ya maka shahararren mawakin zamanin nan, Tuface Idibia da matarsa, Annie Macaulay kotu, inda ya bukaci a biya shi diyyar Naira miliyan N120 saboda aikin daukar hotunan da ya yi a yayin bikin auren mawakin. Mai hoton dai ya yi ikirarin cewa an dauke shi kwantaragin aikin hoton, a yayin bikin aurensu na gargajiya da aka gudanar a watan Maris na bana, a Jihar Akwa-Ibom, inda bayan ya kammala aikin aka ki biyansa ijararsa.
Okolo, wanda ke gudanar da sana’arsa ta daukar hoto a Abuja, ya yi ikirarin cewa wata ta kusa da mawakin ce mai suna Chineze Anyaena ta dauki hayarsa domin ya dauki hotunan, a yayin bikin auren a Akwa-Ibom. Ya kara da cewa, tun da farko har ya so ya ki amsar aikin domin kuwa ba angon ba ne da kansa ya neme shi da aikin, amma ya amince daga baya saboda la’akari da muhmmmancin aikin. Haka kuma, ya ce ita kanta amaryar Tuface, Annie, daga bisani, ita da kanta ta neme shi da ya wanke mata manya-manyan hotuna guda goma. Ya yi kukan cewa ya zuwa yanzu, bayan wata kusan hudu da aikin, amma har yanzu ba a biya shi ko kwabo ba.
An dai gabatar da karar ce a Babbar Kotu da ke Legas, wacce Mai Shari’a Mohammed Idris ya saurara. Za dai a ci gaba da sauraren karar ne a ranar 16 ga watan Oktoba mai zuwa.