Mai intabiyu
Wani mutumi ne ana kiransa Tanimu, ya je intabiyu ya bi layi, sai aka kira na gabansa aka fara yi masa tambayoyi kamar haka: “Mene ne sunan shugaban kasarka wanda ya bar gado?” Ya ce: “Goodluck Jonathan.” Wace shekara Janar Murtala Muhammad ya yi mulki?” Ya ce: “1976.” Shin cutar kanjamau tana da magani?” Ya […]
Wani mutumi ne ana kiransa Tanimu, ya je intabiyu ya bi layi, sai aka kira na gabansa aka fara yi masa tambayoyi kamar haka: “Mene ne sunan shugaban kasarka wanda ya bar gado?” Ya ce: “Goodluck Jonathan.” Wace shekara Janar Murtala Muhammad ya yi mulki?” Ya ce: “1976.” Shin cutar kanjamau tana da magani?” Ya ce: “E, amma likitoci ba su tabbatar ba.” Sai mai tambayar ya ce masa: “Kira mai bi maka.” Tanimu ya fara jin tsoro. Mutumin na fitowa sai ya ce masa: “Don Allah fada mani amsar tambayar.” Mutumin ya ce masa ai ba irinta za a yi maka ba.” Ya ce ya dai fada masa haka nan. Suna kan haka sai mai intabiyu ya ce: “Mutum na gaba ya shigo.” Sai mutumin ya ce wa Tanimu: “Amsar ita ce Goodluck Jonathan, 1976 da kuma E, amma likitoci ba su tabbatar ba. Tanimu ya shiga aka fara tambayarsa kamar haka: “Ya sunanka?” Ya ce: “Goodluck Jonathan.” “Shekarunka nawa?” Ya ce: 1976.” Mai intabiyu ya ji haushi ya ce masa: “Kai mahaukaci ne?” Tanimu ya amsa da cewa: “E, amma likitoci ba su tabbatar ba.”
Daga Nura S. Suleja, 08107575716