Mai jego ta kuɓuta bayan haihuwan tagwaye a hannun barayin daji

Wata mata a Jihar Neja ta tsere daga hannun wasu da suka yi garkuwa da ita bayan ta haifi tagwaye a hannunsu.

Mai jego ta kuɓuta bayan haihuwan tagwaye a hannun barayin daji

Wata mata mai suna Maimuna da ke da zama a garin Lambata na Ƙaramar Hukumar Gurara a Jihar Neja ta samu kuɓuta daga hannun wasu da suka yi garkuwa da ita bayan ta haifi tagwaye a hannunsu.

Matar kamar yadda Aminiya ta samu labari ta hau mota ne daga garin Lambata a kusa da ƙauyen nasu a ranar Alhamis ta makon jiya zuwa Babban Asibitin garin Suleja don yin awu, bayan ta lura da rashin motsawar cikinta.

Ta ce an yi mata awun sannan aka buƙaci ta sake komawa asibitin washegari, ranar Juma’a da nufin aihuwa.

Sai dai a cewarta, bayan shigarta mota a gefen titi da ke kusa da asibitin da nufin komawa gida, ta yi rashin sa’ar faɗawa cikin motar ɓarayi.

Ta ce babu wata magana da ta gudana a cikin motar a tsawon lokacin tafiyar da suka yi, har zuwa shigarsu garin.

“A nan ne na sanar da direba cewa zan sauka a mahaɗar hanya da aka kira Kusa-kusa, inda ya amsa mini da cewa, ya ji.

“Daga nan ban sake sanin inda nake ba, sai bayan wayewar gari inda na gan ni a wani waje tare da ledar ruwan magani a jikina.

“Naquda ta bijoro mini sannan bayan wani lokaci sai na haifi yara maza biyu da misalin qarfe ɗaya na dare a ranar ta Alhamis.

“Na ji kukan yaran amma sai barci ya sake xauka ta. Bayan na sake farkawa a ranar Juma’a da safe, na tambayi wadda take tsaye a kaina wata dattijiya da ke tare da wani saurayi game da yaran da na haifa. Amma sai matar ta ce ai yaran ba nawa ba ne nasu ne, har ta kai ga an mare ni kamar sau uku bayan na matsa kan tambayan yaran.

“Na yi ta kuka, sai na ce su taimaka mini ina son zan yi magana da mijina, amma ba su ce mini komai ba.

“Ina kan gado a wajen kamar dai asibiti ko tashi ba na iya yi sai addu’a na ke ta yi. Can bayan yanayin duhu ya fara sai na ji mutanen waɗanda ke magana da harshen Hausa, suna cewa akwai zama da za a yi da jagoransu wanda ke kan hanya zuwa wajen.

“Na yi amfani da wannar damar na gudu, sai na sami kaina a garin Kagara.

“A can ne na sami mota da za ta wuce da ni zuwa garin Minna, kuma mai motan ne ya taimaka mini ya tsaya a wani asibiti da ke wani qauye aka yi mini allura inda jinin da ke zubo mini ya ragu.

“Mun ci gaba da tafiya, sai dai bayan mun isa garin Zungero sai muka sami labarin cewa a kwai ɓarayi sun tare hanya gta gaba.

“Haka muka juya muka sake komawa garin Kagara, a can ne a ka kwantar da ni a wani asibiti tare da ɗaura ni a kan ruwan leda da kuma ba ni magunguna.

“Direban ya taimaka mini matuƙa ya haɗa ni da wasu danginsa da ke garin.

“Bayan sallama ta ne na wuce zuwa Garin Minna, in ji matar wadda ta zanta da gidan rediyon Prestige da ke Garin Minna.

Aminiya ta tuntuɓi kwamandan ƙungiyar ’yan sintiri na ƙaramar hukumar Gurara da ke Jihar Neja, Malam Abdullahi Bello a shekaranjiya Laraba, inda ya sanar da cewa bayan sun sami labarin, sun tattauna a kan lamarin a yayin zamansu da ya shafi yankin Masarautar Suleja ba ki ɗaya.

Ya ce sun yanke shawarar ziyartar matar wadda ya ce ke wani asibiti da ke garin Minna, don ji daga bakinta.

Da aka tuntuɓe shi, babban jami’in hulɗa da jama’a ta rundunar ’yan sanda a jihar Neja, S.P Wasiu Abiodun ya ce zai yi bincike a kan lamarin.