Mai jiran gadon sarautar Ibadan ya kwanta dama
Rasuwar Balogun na Ibadan, Cif Sulaiman Adegboyega Alao Omiyale, wanda ke jiran hawa gadon sarautar Ibadan ta samar da gurbi mai saukin cikewa ba tare da jayayya a masarautar Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11 ba.Marigayin mai shekaru 91 ya rasu ne a ranar Asabar a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan. Babban Limamin Ibadan […]
Rasuwar Balogun na Ibadan, Cif Sulaiman Adegboyega Alao Omiyale, wanda ke jiran hawa gadon sarautar Ibadan ta samar da gurbi mai saukin cikewa ba tare da jayayya a masarautar Ibadan mai kunshe da kananan hukumomi 11 ba.
Marigayin mai shekaru 91 ya rasu ne a ranar Asabar a Asibitin Koyarwa na Jami’ar Ibadan. Babban Limamin Ibadan Sheikh Abdul Ganiyu Abubakar Agbotomokekere, shi ne ya jagoranci dimbin Musulmi da suka yi masa jana’iza kuma aka binne shi a fadar Ope Agbe gidan Omiyale a unguwar Oja Oba da ke tsakiyar birnin Ibadan a Lahadin da ta gabata.
A tsarin sarauta shi ne mutum na biyu a cikin jerin masu rike da manyan sarautu a masarautar Ibadan. Shi ne zai zama sabon Olubadan idan wanda ke kan gado ya riga shi mutuwa.
daruruwan mutane musamman zuriyar gidan Omiyale maza da mata da suka halarci wajen jana’izar marigayin sun yi ta kuka da hawaye domin nuna juyayin wannan babban rashi da subucewar damar zama Sarki, wato Olubadan na Ibadan idan da yana raye.
Wakilinmu ya tuntubi daya daga cikin manyan mutane dake cikin jerin sunayen masu jiran hawa gadon sarautar Ibadan, Sanata Lekan Balogun, a game da wanda zai maye gurbin marigayi Balogun na Ibadan, sai ya ce: “Ba zan yi wata magana a kan wannan al’amari a yanzu ba amma ina tabbatar maka cewa, abu ne mai sauki da za mu yi cikakken bayani nan da mako biyu masu zuwa.”
Tsarin hawa gadon sarautar Ibadan yana farawa ne daga jagoran zuriyar gida wato ‘Mogaji’ kamar yadda marigayi mai jiran zama Olubadan idan yana raye ya fara a shekara ta 1967. Haka ya rika samun karin girma daga matakala ta farko zuwa matsayi na biyu da zai iya zama Sarki, idan mutumin da ke kan gado ya riga shi mutuwa. Wannan shi ne ya sa ake samun tsoho mai yawan shekaru a matsayin Olubadan. Kuma hakan ne ya haifar da rashin Fadar Sarki ta dindindin a masarautar Ibadan, a inda duk mutumin da ya zama Olubadan yake gudanar da al’amuransa daga cikin gidan da yake zaune da iyalinsa ba tare da gusawa zuwa ga fadar sarki ba; domin babu irinta a Ibadan. Gwamnatin Jiha ce take yi wa irin wadannan gidaje kwaskwarima da ake mayar da su a matsayin fadar Olubadan.