Mai juna biyu ta haihu a Masallacin Harami

A shafe shekaru masu yawa rabon da a haihu a Masallacin Harami

Mai juna biyu ta haihu a Masallacin Harami

Jami’an kungiya agaji ta Red Crescent a Masallacin Harami

Wata mai juna biyu ta haihu a Masallacin Harami da ke birnin Makkah, inda jami’ai kungiyar agaji ta Red Crescent suka karbi haihuwar.

Karo na farko ke nan a shekaru masu yawa da aka samu wadda ta haihu a Masallaci mafi daraja a Musulunci.

Daraktan kungiyar Red Crescent a birnin Makkah, Dokta Mustafa Baljoun, ya ce kafin wayewar garin Litinin matar wadda ’yar kasar Sudan ce ta haihu a Masallacin Harami.

Ya bayyana cewa da misalin karfe 12 na dare matar ta fara jin ciwon mara, a kusa da wani otel da ke makwabtaka da Masallacin Harami, inda jami’an kungiyar suka kai mata dauki, amma sai suka gano cewa nakuda ce kuma a kowane lokaci za ta iya haihuwa.

Kafin su yi wata-wata har ruwa ya fashe, kan jaririn na yunkurin fitowa, shi ne suka shigar da ita motar daukar marasa lafiya, kuma cikin ikon Allah ta haihu lafiya.

Dokta Mustafa ya ce daga baya an kai dauki jegon da jaririnta Babban Asibitin Ajya, inda bayan likitoci sun duba su, suka tabbatar cewa dukkansu suna cikin koshin lafiya.

Ya shawarci masu zuwa Masallacin Harami kan muhimmancin kiran lambar gaggawa ta jami’an kiwon lafiya, ta hanya kiran lambar 997 ko kuma ta amfani da manhajar Asefni ko Tawakkalna.

Ya ce, duk wanda mutum ya yi amfani da shi, jami’an lafiya za su ga inda yake ta taswirarsu, su zo inda yake kai-tsaye su bayar da kulawar da ta dace.