Mai juna-biyu, yara 3 da wasu mutum 15 sun kone a hatsarin tankar mai

Tankar man ta yi bindiga yayin da mutane ke tsaka da dibar mai.

Mai juna-biyu, yara 3 da wasu mutum 15 sun kone a hatsarin tankar mai

Wata tankar mai da ta kama da wuta

Wata mata mai juna biyu da yara uku na daga cikin wadanda suka kone kurmus lokacin da suke kokarin dibar man fetur daga wata tanka da ta kife a garin Ore da ke Karamar Hukumar Odigbo ta Jihar Ondo.

An ce hatsarin ya faru ne a ranar Lahadi, inda motar ta yi bindiga lokacin da wadanda abin ya shafa suke rubibin dibar mai daga tankar da ta yi hatsari.

Wasu majiyoyi da dama sun shaida cewa gobarar ta tashi ne biyo bayan tartsatsin wuta daga motar.

Wani da ya bayyana kansa a matsayin Bamidele, mai tireda a yankin, ya ce tun da farko masu ababen hawa sun gargadi wadanda abin ya shafa da kada su je kusa da tankar.

Ya ce, “Ina kokarin sallamar wani kwastoma sai na hangi direban babbar motar na kokarin wuce wata mota sai motar ta kwace masa. Hakan ya sa jama’a suka shiga jidar mai da jarkoki.

“Wasu direbobi da fasinjoji da suka ga abin da ya faru har sun gargade su da kada su je kusa da motar amma suka ki. Nan take motar ta yi bindiga. Daga baya ne muka ji cewa wayar salula ce ta daya daga cikin wadanda abin ya shafa ta haddasa wutar.

“Wata mata mai juna biyu, kananan yara uku da wasu fiye da 15 sun mutu lokacin motar ta yi bindiga.”

Bamidele ya kara da cewa Hukumar Kiyaye Hadura ta Kasa (FRSC), ta kwashi gawarwakin wadanda suka mutu da wadanda suka ji rauni zuwa asibitin gwamnati.

Kwamandan hukumar a Jihar, Ezekiel Son-Allah, ya tabbatar da faruwar lamarin a wata hira da manema labarai, inda ya ce wadanda suka tsira da ransu suna karbar magani a sashen kuna na asibitin.

Haka kuma Kakakin ’yan sandan Jihar, Funmilayo Odunlami-Omisanya, ta ce wasu daga cikin wadanda abin ya shafa sun kone ba tare an gane su ba.

Odunlami-Omisanya ta kara da cewa an ajiye wadanda suka rasu a dakin ajiye gawa na asibitin.