Mai kai wa ’yan bindiga karuwai ya shiga hannu

Kawalin ya bayyana yadda yake kai wa ’yan bindiga makamai da karuwai da miyagun kwayoyi da ma’aikatan lafiya a duk lokacin da suke bukata

Mai kai wa ’yan bindiga karuwai ya shiga hannu

Wani wanda yake kai wa ’yan bindiga karuwai domin yin lalata da su ya shiga hannun jami’an tsaro.

’Yan sanda sun bayyana cewa kawalin ya kuma kware wajen yin safarar makamai ga kungiyar jagoran ’yan bindiga mai suna Ardo, wanda ake nema ruwa a jallo a yankin Kagarko da ke Jihar Kaduna.

An kuma gano cewa mutumin wanda yake harkar hada-hadar tura kudi ta PoS, shi ke kai wa iyalan ’yan bindiga kudade a yankin na Kagarko.

Dubun kawalin ta cika ne a yayin wani samamen hadin gwiwa da ’yan sanda suka gudanar a yankin.

Kwamishinan ’Yan Sandan Birnin Tarayya, ya sanar ranar Talata cewa wanda ake zargin ya shaida musu cewa shi ke tsara yadda ake kai wa ’yan bindiga karuwai da miyagun kwayoyi da ma’aikatan lafiya a duk lokacin da suke bukata.

“Ya kuma amsa cewa yana yin dakon kudi tare da rabawa ga iyalan ’yan bindiga.

“A cewarsa, kudaden da ya raba wa iyalan ’yan bindiga sun haura Naira miliyan ashirin,” in ji kwamishinan ’yan sandan.

Igwe ya ce wanda ake zargin ya tabbatar musu cewa ’yan bindigar da ke karkashin Ardo sun kai 15 kowannensu da bindiga kirar AK-47.

DSS ta gurfanar da Mahdi Shehu kan zargin ta’addanci

Sojoji sun kashe mataimakin Bello Turji

Harin ’Yan Fashi: Buni ya jajanta wa ’yan kasuwar Ngalda

An saki matar Ekweremadu daga gidan yari a Birtaniya, ta dawo Najeriya