Mai kai wa ’yan ta’adda kakin sojoji ya shiga hannu a Kaduna

’Yan sanda sun harbe wani ɗan fashi da makami har lahira tare da kama wani mai kai wa ’yan bindiga kakin sojoji

Mai kai wa ’yan ta’adda kakin sojoji ya shiga hannu a Kaduna

Yan sanda sun harbe wani ɗan fashi da makami har lahira tare da kama wani mai kai wa ’yan bindiga kakin sojoji a Jihar Kaduna.

Mai yi wa ’yan bindigar safarar kakin sojojin ya masa cewa yana kai musu yadin kakin ne a cikin daji domin su dinka da kansu a Dajin Jihar Neja.

Shi kuma dan fashin da ’yan sanda suka kashe, sun ƙwato bindiga kirar gida da harsasai a hannunsa a lokacin rundunar ta kai farmaki kan gungun ’yan fashin da ke ƙoƙarin tafka ta’asarsu.

Kakakin rundunar ’yan sanda a Jihar Kaduna, ASP Mansur Hassan, ya ce rundunar ta kuma kama ɓarayin mota biyu da ake zargin kuma su ma sun amsa laifinsu.

Ya ce a ranar Lahadi da misalin karfe 1.20 na rana ’yan sanda da ke sintiri a kan hanyar Kaduna zuwa Birnin Gwari suka kama wani mutum da kayan sojoji har na mutum 15 a cikin baƙar leda.

Wanda aka kama da kayan na sojojin ya tabbatar da cewa zai kaiwa Wani mutum ne a garin Udawa domin ya Kai wa ’yan ta’adda a dajin Chukuba da ke Karamar Hukumar Shiroro ta Jihar Neja domin su ɗinka.

Jami’in ya ce wanda ake zargin yana ba jami’an tsaro hadin kai a binciken da suke gudanarwa domin kamo sauran abokan ta’addancinda da ke daji.

 

A ranar Talata kuma ’yan sanda da ke yankin Makarfi da misalin karfe 12 na dare sun yi kicibis da gungun ’yan fashi da makami da suka tare hanya da manyan itatuwa da kuma manyan duwatsu.

Isarsu wurin ke da wuya sai aka fara musayar wuta, amma Jami’an ‘yan sanda suka fatattaki ‘yan fashin inda suka ranta a na kare tare da raunukan harbi.

Rundunar ta ce Wani mutum ne ya kai sanarwar sace motarsa kirar Toyota amma jami’an suka gano motar a Hayin Dan Mani da ke Kaduna da wasu mutane biyu da ake zargin.

An kuma kama wasu mutum biyu daga Kano da mota kirar Marsandi wadda ake zargin ta sata ce.

Ya ce a lokacin da ake gudanar da bincike dukkan wadanda ake zargin sun amsa cewa sun aikata laifin da ake zargin su.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Kaduna Audu Ali Dabigi ya yaba wa jami’an rundunar bisa yadda suke jajircewan tare da daukar matakin da ya dace a lokacin ake bukatarsu