Mai Kaltungo ya bukaci Gwamnan Gombe ya hada kai da kwararru don koya wa matasa kere-kere

Mai Kaltungo da ke Jihar Gombe, Injiniya Saleh Muhammad, ya bukaci Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ya nemi hadin kan kwararru a bangaren kere-kere su koya wa matasa kera murhunan zamani da za su sa a rage amfani da itace wajen girki, domin kauce wa kwararowar hamada da sare itatuwa ke jawo ta.Injiniya […]

Mai Kaltungo ya bukaci Gwamnan Gombe ya hada kai da kwararru don koya wa matasa kere-kere
Mai Kaltungo ya bukaci Gwamnan Gombe ya hada kai da kwararru don koya wa matasa kere-kere

Mai Kaltungo da ke Jihar Gombe, Injiniya Saleh Muhammad, ya bukaci Gwamnan Jihar Gombe Alhaji Ibrahim Hassan dankwambo ya nemi hadin kan kwararru a bangaren kere-kere su koya wa matasa kera murhunan zamani da za su sa a rage amfani da itace wajen girki, domin kauce wa kwararowar hamada da sare itatuwa ke jawo ta.
Injiniya Saleh Muhammad, ya bayyana haka ne a lokacin da ya jagoranci tawagar Sarakunan Jihar zuwa gidan gwamnatin domin gaisuwar karamar Sallah ga Gwamnan inda ya koka kan yadda ake fuskantar kwararowar hamada a yankinsa da hakan ya yi sanadin lalata shukar da al’ummar yankin suka fara yi.
Ya ce murahun zamanin da ba su bukatar itace mai yawa za su taimaka ga rage sare itatuwa kuma hakan zai taimaka wajen rage kwararowar hamadar.
Ya jinjina wa Gwamna dankwambo kan yadda ya taimaka wajen yakar ta’addancin Boko Haram da a shekarun baya suka hana gudanar da hawa da bikin Sallah a jihar.
Mai Kaltungo wanda shi ne Mataimakin Shugaban Majalisar Sarakunan Jihar ya roki Gwamna da ya ceto manoman jihar daga hannun ’yan kasuwa da suke sayar musu da taki da tsada, musamman dabararsu ta kin sayar wa manoma marasa karfi taki sai dai su ba su buhun taki daya da kaka su biya da masara.
Da yake maida jawabi Gwamna Ibrahim dankwambo, ya gode wa sarakunan ya yi kan gaisuwar Sallar, sannan ya hori al’ummar jihar da kada su mike kafa saboda an samu tsaro, yana da kyau su ci gaba da sa ido tare da kai rahoton duk wani abu da ba a yarda da shi ba ga hukumomin tsaro.
Dangane da takin zamani ya ce yanzu haka gwamnatinsa ta yi odar tan dubu 20, kuma akwai tan dubu 15 a hannu da za a kaddamar da sayar da shi ga manoma a makon gobe.