Mai Kamfanin Facebook na fuskantar matsin lamba

Shugaban Kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan bukatar ya bayyana kansa domin a bincike shi bisa zargin da ake yi wa shafin nasa na kin shaida wa masu amfani da shi cewa ana tattara bayanan da suka sanya a shafukansu da kuma ajiye su a wani kamfanin sadarwa na […]

Mai Kamfanin Facebook na fuskantar matsin lamba

Shugaban Kamfanin Facebook, Mark Zuckerberg na ci gaba da fuskantar matsin lamba kan bukatar ya bayyana kansa domin a bincike shi bisa zargin da ake yi wa shafin nasa na kin shaida wa masu amfani da shi cewa ana tattara bayanan da suka sanya a shafukansu da kuma ajiye su a wani kamfanin sadarwa na Cambridge, wanda ya taka rawa wajen taimaka wa Donald Trump lashe zaben Shugaban kasar Amurka a shekarar 2016.

A makon jiya ne Facebook ya ce ya toshe kamfanin Cambridge Analytica daga shafin, yayin da yake bincike kan korafin cewa kamfanin mai cibiya a Landan bai goge bayanan da ake zargi ya samu ta hanyar karya ka’idojin Facebook ba kamar yadda ya yi alkawari. Dukan kamfanonin biyu dai Cambridge Analytica da Facebook sun yi watsi da batun cewa sun aikata ba daidai ba.

Tuni hannayen jarin Facebook suka fara yin kasa sakamakon matsin lambar da yake fuskanta. Duk da alwashin da ya sha a shekarar 2018 cewa zai gyara kamfanin nasa, Mark Zuckerberg ya yi kokarin kauce wa sukar da yake sha daga dimbin mutane maimakon haka sai ya yi ta aike lauyoyi zuwa kwamitoci domin sauraron korafe-korafe.

Haka an wallafa kalaman Zuckerberg na baya-bayan nan a kan wasu ce-ce-ku-cen da ke faruwa kan Facebook a wani kebabben shafin Intanet, sannan aka wallafa a shafinsa na Facebook. Yayin da ake kara nuna damuwa kan yadda bayanan da Facebook ke tatattarawa za su kara iza wutar farfagandar siyasa, wadansu manyan masu fada-a-ji a karshen wannan makon sun ce lokaci ya yi da Mista Zuckerberg zai fito fili ya kare kansa kan wannan batu.

Sannan wadansu ma sun yi kira da a yi bincike kan ko kamfanin na Facebook ya karya wasu dokoki na tattara bayanai da kuma dokokin rashin samun izinin masu amfani da shafin kafin tattara bayanan da suka shafe su.