Mai kanjamau ya yi lalata da mata bakaken fata sama da 600 don yada ta
Wani saurayi dan kasar Amurka mai suna Jason Pope da aka fi sani da DJ Kid, da ke dauke da cutar kanajmau mai karya garkuwar jiki ya shiga hannun ’yan sandan Amurka saboda zarginsa da laifin yin lalata da mata sama da 600 bakaken fata da nufin yada cutar ta kanjamau. Jason Pope, ya wallafa […]
Wani saurayi dan kasar Amurka mai suna Jason Pope da aka fi sani da DJ Kid, da ke dauke da cutar kanajmau mai karya garkuwar jiki ya shiga hannun ’yan sandan Amurka saboda zarginsa da laifin yin lalata da mata sama da 600 bakaken fata da nufin yada cutar ta kanjamau.
Jason Pope, ya wallafa hotunan wadansu mata da ya yi lalata da su a kafafen sada zumunta na zamani.
An kama Jason, bayan hukumomin tsaron Amurka sun tabbatar ya yi lalata da mata sama da 600 da yanzu aka tabbatar suna dauke da cutar.