Mai kiwon doki ya zama shahararren dan kwallon polo
kwallon dawaki (Polo) wasa ne na masu hannu da shuni da yake tattare da matukar hadari. Da farko Malam Ibrahim Muhammad, wanda aka fi sani da dangaye, mai kiwon doki ne, amma yau da kullum, wadda take tare da shauki, ta sa ya zama shahararren dan kwallon dawaki, domin ta kai har yana buga wa […]

kwallon dawaki (Polo) wasa ne na masu hannu da shuni da yake tattare da matukar hadari.
Da farko Malam Ibrahim Muhammad, wanda aka fi sani da dangaye, mai kiwon doki ne, amma yau da kullum, wadda take tare da shauki, ta sa ya zama shahararren dan kwallon dawaki, domin ta kai har yana buga wa kungiya.
Ya ci fiye da kofunan zinari 12, kuma ya wakilci Najeriya a gasar cin kofin kwallon dawaki ta duniya.
Aminiya ta sami ganawa da shi, inda ya bayyana mata sirrin da ya kai shi wannan matsayi da wasu daga cikin irin gwagwarmayar da ya sha, a cikin lamarinsa na kiwon doki da kuma wasan polo.
Mahaifinsa shi ne Alhaji Muhammadu Mustapha Babayo, daya daga cikin dattijan Unguwar Doki da ke gundumar Unguwar Sarki a Kaduna. Ya gaji aikin kiwon dawakan Polo ne daga gurin mahaifinsa, lamarin da ya hada da zuwa makarantun addini da na boko.
Tauraruwarsa ta fara haskawa ne yayin da ya zama cikin na farko da suka fara wasan a kan basukur (watau keke). A lokacin matasa ne kan yi wasan a kan keke don kayatar da sarakuna da masu hannu da shuni da janar-janar da manyan sojoji da dai sauran manyan baki, a yayin gasar ta shekara-shekara da akan yi a filin sukuwa na Kaduna.
Burin Ibrahim dangaye ta fara cika ne yayin da mahaifinsa ya saya masa dawakai don su ba shi damar fara yin wasan gadan-gadan, don ba wanda zai ba shi dawakansa ya hau siddan. Sai ma daga baya ne masu dawakan suka tallafa wa masu yi musu kiwo wajen ba su izinin hawan dawakan don buga wasan polo
Hazakar Ibrahim Muhammad ta kai har ya fara wasan kwallon doki, bayan ya sami ilimin ka’idodijin wasan ciki-da-bai, lamarin da ya sa ya zama shahararren dan wasan polo da kungiyar El-Amin da ke Minna, sannan kuma ya buga wa Najeriya wasa a gasar kwallon polo na cin kofin duniya.
Ibrahim ya ce wasan farko da ya yi a matsayin shahararren dan wasan polo shi ne wanda ya buga don cin kofin Tedtile, wanda suka lashe. Sannan ya jagoranci cin babban kofin Georgian da na Sardauna. Sannan kuma ya buga wa Najeriya wasa a gasar cin kofin duniya a shekarar 2011 a kasar Malaysia.
Burin duk dan kwallo, kowane iri, shi ne lokacin da zai sa hannu don karbar cekin kudi don fara wasan kwararru. Ibrahim dangaye ya sa hannun buga wasan kwarewa ne da kungiyar El-Amin da ke Minna, Jihar Neja, inda har yanzu yake wasa da su, har ya kai matsayin (+3), alhalin wanda ya fi kowa shahara a kwallon polo a Najeriya shi ne Alhaji Bello Buba da ke da matsayin (+4).
Ibrahim dangaye, wanda ya koma ya zama mai ziyartar masu yi masa kiwo, sannan ya duba matsayin dawakansa, yana ba matasa shawarar su nemi il’mi, su guji shaye-shaye, su zama mutanen kwarai, ba ’yan na baya ga dangi ba.
A karshe ya yi fatar ganin barakar da ta dabaibaye wasan polo, a kungiyance, za ta samu an dinkuwa, ta yadda kungiyoyin polo na NPA da NPF, za su dayo tsintsiya madaurinki daya.
Turawa ne dai suka fara wasan kwallon dawaki a Arewacin Najeriya a filin sukuwa da aka fi sani da Dandalin Murtala Muhammad da ke Kaduna da kuma sauran yankunan kasar nan. Marigayi Sarkin Katsina, Sa Muhammadu Dikko ya fara rungumar wasan gadan-gadan, har ya kawo matsayin da yake a yau.